Matar aure ta bar mijinta don auren ɗan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'

Matar aure ta bar mijinta don auren ɗan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'

- Mata mai shekaru 35 ta yi wuff da dan mijinta mai shekaru 21 bayan rabuwa da mahaifinsa

- Marina Balmesheva ta bayyana cewa har tiyata ta yi domin yi wa wasu sassan jikinta kwaskwarima

- Ta ce ita ce ke kula da dawainiyarsu a halin yanzu kafin sabon mijinta ya kafu da kafafunsa ya rika bada gudunmawarsa

Wata mata ra rabu da mijinta ta auri dan sa mai shekaru 21 kuma ta amsa cewa an yi mata tiyata ta kwaskwarima domin ta kara kyau, LIB ta ruwaito.

Marina Balmesheva, mai shekaru 35, wata mai rubutu a kan motsa jiki, tana dauke da juna biyu wa dan mai suna Vladimir kuma ta nemi su tafi kotu suyi yarjejeniya domin tabbatar da ba za ta rasa kadarorinta ba.

Matar aure ta bar mijinta don ta kasance da dan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'
Matar aure ta bar mijinta don ta kasance da dan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

Marina ta san saurayinta na yanzu tun yana da shekaru bakwai da haihuwa a duniya.

Duk da cewa ta taba auren mahaifinsa, ta ce bata taba ganin mutum, "kyawawan idanu irin nasa ba a duniya."

Tsohon mijinta, wadda suke da yara biyar tare, ya ce ta yi wa dansa dabara ne ta aure shi.

DUBA WANNAN: Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

Matar aure ta bar mijinta don ta kasance da dan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'
Matar aure ta bar mijinta don ta kasance da dan shi, ta kara da yin 'kwaskwarima'. Hoto: @lindaikeji
Source: Twitter

"Bai taba yin wata budurwa ba kafin ita," in ji shi.

"Ba su jin kunyan kwanciya tare a lokacin da na ke gidan.

"Idan da ba yaro na bane, da na yafe mata cin amanar da ta yi min ...

"Bayan hakan tana dawo wa gadon mu ta kwanta tamkar ba abinda ya faru."

Sai dai Marina ta ce aurenta na farko kawai, "rayuwa ce ta yaudara"

Ta shaida wa masu bibiyar shafinta a yanar gizo 500,000: "Shin na yi nadamar tarwatsa gida? Eh da a'a.

"Na ji kunyar cewa na tarwatsa gida.

"Shin ina son koma wa tsohon miji na? A'a. Ina fushi da shi har yanzu? A'a.

"Mutum ne na gari kuma yana kulawa da yaran mu ...

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace yaran shugaban APC a Zamfara, sun nemi a basu N50m

Ta yaya yaran mu suka yi maraba da sabon sauyin? Ba su damu ba.

Mene ya sauya a rayuwa yanzu? Ina da aure. Na dawo babban birni. Ina kauna kuma ana kauna ta."

Amma akwai yiwuwar kamar soyayyar ta da dan mijinta ba zai dade ba.

"Yanzu ya fara natsuwa a rayuwarsa," in ji ta.

Ta cigaba da cewa ya fahimci matsayinsa yanzu cewa itace ta siya motarsu ta farko ta kuma biya kudin gidan da suke zaune.

Kazalika, ta ce ya san abinda ya ke yi kuma ta yi tiyata don yin kwaskwarima a wasu sassan jikinta domin ta kara kawata masa kanta.

A hotunan da ta wallafa, shekarun ta 32-35 amma a watan Fabrairun 2020 za ta cika shekaru 36 kuma bai damu da hakan ba a cewarta.

A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel