AFCON: Tinubu Ya Aika Muhimmin Sako Ga Super Eagles Bayan Ta Yi Rashin Nasara a Wasan Karshe

AFCON: Tinubu Ya Aika Muhimmin Sako Ga Super Eagles Bayan Ta Yi Rashin Nasara a Wasan Karshe

  • Duk da sun sha kasa a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON), Shugaba Tinubu ya jinjinawa tawagar Super Eagles ta Najeriya
  • Shugaba Tinubu, ta hannun Ajuri Ngelale ya jaddada cewa tawagar Najeriya ta samu gagarumar nasara a zukatan Afirka da ma duniya baki daya
  • Ya kuma yi nuni da cewa rashin daukar kofin ba zai karya guiwar 'yan kasar ba, "sai dai ya kara mana himma da tunkarar wasannin gaba"

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Najeriya bisa jajircewar da suka nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023 a kasar Cote d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya shilla kasar waje don shajja'a Super Eagles a wasan karshe na AFCON 2023

Shugaba Tinubu ya yabawa tawagar, kocin, ma’aikatan tawagar, da daukacin hukumar gudanarwa bisa kwazon da suka yi, da sadaukarwar da suka yi a wannan gasa.

AFCON: Tinubu ya jinjinawa tawagar Super Eagles
AFCON: Tinubu ya jinjinawa tawagar Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe. Hoto: @PBATMediaCentre, @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi farin ciki, yana mai jaddada cewa mun samu gagarumar nasara a zukatan Afirka da ma duniya baki daya ta hanyar dagewarmu da jajircewa a fagen wasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar.

Ya ce:

“Wannan abin da ya faru ba zai karya mana guiwa ba, sai dai ya kara mana himma, kuma tabbas gwamnatina tana nan don ganin wannan burin namu ya zama gaskiya.”
"Mu al'umma ce mai girma da tutiya da tutar kore-fari-kore da ke alamta juriya, farin ciki, bege, aiki tukuru, da nuna ƙauna babu gajiyawa."

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Karanta sanarwar a kasa:

AFCON 2023: Najeriya ta sha kaye a hannun Cote d'Ivoire

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, tawagar Najeriya ta sha kaye a hannun Cote d'Ivoire a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023.

An tashi wasan ne da ci 2 da 1, bayan da Najeriya ta fara zura kwallon farko amma Cote d'Ivoire ta rama tare da yin kari a zagayen wasan na biyu.

A yanzu dai Cote d'Ivoire ta daga kofi yayin da Najeriya ta zo na biyu sai kuma kasar Afrika ta Kudu ta zo ta uku, yayin da DR CONGO ta zo ta hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel