Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Ƙarshen da Najeriya Zata Fafata da Ivory Cost

Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Ƙarshen da Najeriya Zata Fafata da Ivory Cost

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gasar cin kofin mahiyar Afirka (AFCON) na dab da ƙarƙarewa yayin da aka shirya murza leda a wasan ƙarshe ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024.

Tawagar ƴan wasan Super Eagles ta Najeriya zasu fafata da tawagar Côte d’Ivoire a wasan ƙarshe domin tantance zakaran gasar AFCON 2023, The Nation ta ruwaito.

Wasan karshe a gasar AFCON.
Muhimman Abubuwa 12 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Wasan Najeriya da Ivory Coast Hoto: Super Eagles
Asali: Getty Images

Masu masaukin baƙi sun samu tikitin zuwa wasan ƙarshe ne ranar Laraba da daddare bayan lallasa Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Congo da ci 1-0 mai ban haushi.

Super Eagles ta tsallake zuwa wasan ƙarshe ne bayan ta doke Afirka ta Kudu da ci 4-2 a bugun fenariti mai ban sha'awa.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin abubuwa 12 da ya kamata ku sani kan wasan karshe

1. An tsara buga wasan ƙarshe a gasar cin kofin AFCON 2023 idan Allah ya kaimu ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024 da misalin ƙarfe 9:00 na dare agogon Najeriya.

2. Za a ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika 2023 a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, Ivory Coast, wanda aka fi sani da filin Olympic Stadium of Ebimpe.

3. Wannan filin wasa yana ɗaukar ƴan kallo 60,000 kuma shi ne filin ƙwallo mafi girma a ƙasar Côte d’Ivoire.

4. Za a haska wannan wasa da Najeriya zata kara da Ivory Coast a tashoshin Sky Sports Main Event, Sky Sports Football, Sky Sports Premier League, Sky Sports Ultra HDR, BBC Three, BBC iPlayer da BBC Sport a Burtaniya.

Kara karanta wannan

AFCPN 2023: Kocin Cote d'Ivoire ya fadi hanyar da za su bi don doke Najeriya a wasan karshe

5. Najeriya ta doke Ivory Coast a kan hanyarta ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka guda biyu cikin uku da ta ɗauka a tarihi (1994, 2013).

6. Duk ƙasar da ta ɗauki kofin a wannan shekara zata samu kyautar kudi dala miliyan 7 (N9bn).

7. Waɗanda suka zo na biyu kuma zasu samu kyautar kudi dala miliyan hudu.

8. Har kawo yanzu kwallaye biyu aka zura a ragar Najeriya tun farkon fara gasar yayin da masu tsaron gidan Ivory Coast suka yi sake aka jefa musu kwallo 8 a wasa 6.

9. Najeriya da Ivory Coast sun buga wasa a rukuni guda, kuma wasan ƙarshen da za a buga zai shiga cikin wasannin da aka buga tsakanin ƙasashen da suka fito daga rukuni ɗaya.

10. Ivory Coast dai ita ce kasa ta farko mai masaukin baki da ta kai wasan karshe na gasar cin kofin Afrika tun bayan ƙasar Masar a 2006.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana

11. Najeriya zata kara a wasan karshe na gasar AFCON karo na takwas kuma kasashen Masar da Ghana (da suka buga 9) ne kaɗai suka wuce Super Eagles.

12. Karo huɗu da ƙasar Ivory Coast ta kai wasan ƙarshe an tashi ne kurman duro watau babu wanda ya leƙa zaren abokin karawarsa, inda aka buga Firaneti.

Sun ci biyu daga cikin bugun daga kai sai mai tsaron gida (1992 da 2015, duka da Ghana) sannan suka sha kashi biyu (2006 vs Egypt da 2012 vs Zambia).

Ahmed Musa na shirin kafa tarihi

A wani rahoton kuma yayin da Najeriya ke shirin karawa da masu masaukin baƙi a wasan karshe ranar Lahadi, ƴan wasa biyu zasu kafa tarihi idan Super Eagles ta yi nasara.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya na fatan lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) karo na huɗu a tarihi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262