Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu Ba Zai Halarci Wasan Karshe Na AFCON Ba, Bayanai Sun Fito

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu Ba Zai Halarci Wasan Karshe Na AFCON Ba, Bayanai Sun Fito

  • Shugaba Bola Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshe na AFCON
  • Tinubu ya ba da umarnin goyon bayan Super Eagles yayin da za su fafata da ƙungiyar The Elephants ta Cote d'Ivoire a ranar Lahadi, 11 watan ga Fabrairu
  • Shugaban ya buƙaci ƴan Najeriya da su nuna cikakken goyan baya wanda zai kai ga nasarar Super Eagles

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Fadar shugaban ƙasa, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ba tsakanin Super Eagles da ƙungiyar The Elephants ta Cote d’Ivoire.

Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshe na AFCON, a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

Tinubu ya tura Shettima zuwa Cote d'Ivoire
Shugaba Tinubu ba zai halarci wasan karshe na AFCON ba Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yada labarai da sadarwa ya bayyana hakan a wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba da shawara na musamman kan Labarai da dabaru ga Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, shi ma ya tabbatar da hakan ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa kasancewar mataimakin shugaban ƙasa Shettima a wasan ƙarshen tare da tawagar, alama ce ta nuna goyon bayan gwamnati ga ƙungiyar da kuma jajircewa domin nasararsu."

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga ƴan Najeriya da su haɗa kai domin marawa Super Eagles baya.

Shugaban ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara zage damtse wajen ƙarfafa gwiwa tare da haifar da kishin ƙasa wanda zai sa ƙungiyar ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana

Karanta wasu abubuwa kan AFCON 2023

Hanyar Doke Najeriya a Wasan Karshe Na AFCON

A wani labarin kuma, kun ji cewa kocin ƙungiyar The Elephants ta ƙasar Cote d'Ivoire ya yi magana kan hanyar doke Najeriya a wasan ƙarshe na AFCON 2023.

Emerse Fae ya bayyana cewa za su yi nazarin salon wasan Super Eagles domin yin nasara a kansu a wasan na ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel