FAAC: Yadda Aka Rabawa Gwamnoni da Ministan Abuja Naira Tiriliyan 6.5 a Shekara 1

FAAC: Yadda Aka Rabawa Gwamnoni da Ministan Abuja Naira Tiriliyan 6.5 a Shekara 1

  • An raba sama da Naira tiriliyan 6 daga asusun tarayya na FAAC daga Junairu zuwa Disamban 2023
  • Daga kason FAAC ne gwamnoni da kananan hukumomi su ke samun kudi bayan harajin da aka karba
  • Jihohi masu arzikin danyen mai sun fi tashi da kaso mai tsoka domin ana yi masu karin 13% dabam

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A kowane wata, kwamitin FAAC da ke aikin rabon kudi ya kan zauna domin yin kason abin da gwamnatin Najeriya ta samu.

Ana raba wannan kudi tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kananan hukumomi.

Gwamnoni
FAAC: Wasu Gwamnonin jihohi a 2023 Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

An yi rabon N6.57tr a FAAC

A wani rahoto da aka samu daga The Cable, an yi bayanin abin da kowace jiha ta tashi da shi daga kason N6.57tr da aka raba a 2023.

Kara karanta wannan

Watanni da sauka, masani ya tona yadda Buhari ya jefa Tinubu a ramin tashin Dala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ake ba 52.68%, sai a rabawa gwamnatocin jihohi 26.72%, a karshe kananan hukumomi 774 su na samun 20.60%.

Kudin jihohi masu arzikin mai

Jihohin da ke da arzikin danyen mai su kan samu karin 13% idan an raba kudi a FAAC. Duka jihohin nan suna kudancin kasar ne.

Jaridar ta ce Delta ta samu N483bn a shekarar bara, yayin da Ribas ta zama ta biyu da N426.8bn, sai Akwa Ibom ta karbi N380.10bn.

Kano mai kananan hukumomi 44 ta samu kudi mai yawa duk da ba ta da arzikin fetur. Gombe, Ebonyi da Ekiti kuwa su ne a baya.

Wasu jihohi da yawa ba za su rayu idan aka janye rabon da ake yi daga asusun FAAC ba. Birnin tarayya Abuja ta samu kusan N150bn.

Ga yadda aka yi rabon FAAC a 2023:

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

1 Delta N483.57bn

2 Ribas N426.84bn

3 Akwa Ibom N380.1bn

4 Legas N371.39bn

5 Bayelsa N268.34bn

6 Kano N261.37bn

7 Oyo N207.37bn

8 Katsina N191.43bn

9 Borno N176.94bn

10 Kaduna N170.91bn

11 Jigawa N170.74bn

12 Benuwai N161.99bn

13 Edo N161.69bn

14 Anambra N161.54bn

15 Ondo N156.33bn

16 Neja N155.62bn

17 Imo N152.39bn

18 FCT N145.3bn

19 Sokoto N146.19bn

20 Bauchi N144.98bn

21 Kebbi N143.93bn

22 Osun N141.48bn

23 Adamawa N139.14bn

24 Kogi N136.97bn

25 Enugu N133.29bn

26 Abia N125.92bn

27 Yobe N124.14bn

28 Taraba N123.05bn

29 Filato N121.71bn

30 Ogun N120.72bn

31 Zamfara N119.17bn

32 Kuros Riba N118.8bn

33 Kwara N115.11bn

34 Nasarawa N111.54bn

35 Ekiti N107.5bn

36 Ebonyi N107.45bn

37 Gombe N99.05bn

Ina maganar hako mai a Arewa?

An rahoto Shehu Umar Buba ya ce an yi watsi da kokarin hako danyen mai a yankin Arewacin Najeriya daga rijiyoyin Kolmani.

Sanatan ya zauna da shugaban NNPC, Mele Kyari da NSA, Malam Nuhu Ribadu a kan maganar, za a cigaa da aikin cikin watan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel