Ana Neman Sabun Sabani Tsakanin Gombe da Bauchi kan Mallakar Danyen Mai a Arewa

Ana Neman Sabun Sabani Tsakanin Gombe da Bauchi kan Mallakar Danyen Mai a Arewa

  • Wani Lauya ya fito yana cewa Gombe ta mallaki man da ake shirin hakowa a Arewacin Najeriya
  • Abdullahi Muhammad Tamatuwa yace doka ta tabbatar da rijiyoyin Kolmani sun fada ne a Gombe
  • Tamatuwa yana so Gwamnatin Jihar Gombe ta tashi tsaye, ko kuwa ya kai maganar zuwa kotu

Gombe - An samu Lauya wanda yake zaman kansa, wanda yake yunkurin zuwa kotu kan danyen man da aka yi nasarar ganowa a yankin Arewacin Najeriya.

Aminiya ta rahoto Abdullahi Muhammad Tamatuwa yana barazanar kai maganar gaban Alkali idan har aka mallakawa jihar Bauchi rijiyar man Kolmani.

Wannan Lauya yana ikirarin cewa rijiyoyin nan da za a fara hako danyen man fetur mallakin jihar Gombe ne, ba na makwabciyar ta watau jihar Gombe ba.

Abdullahi Muhammad Tamatuwa mutumin garin Akko ne a jihar Gombe, yace su ne ainihin wadanda suka mallaki rijiyoyin Kolmani ba mutanen Bauchi ba.

Kara karanta wannan

Yayinda Buhari Ke Shirin Kaddamar Da Aikin Hako Mai A Bauchi, Jama'ar Alkaleri Sun Gabatar da Bukatunsu

Laifin shugabannin Gombe ne

An rahoto Lauyan yana zargin shugabannin jihar Gombe tun daga Gwamnoni da aka yi zuwa ‘yan majalisa, da watsi da yankin da rijiyar danyen man yake.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ta sa Barista Abdullahi Tamatuwa yake ganin tamkar an hada baki ne da shugabanninsu domin a mallakawa jihar Bauchi arzikin mutanensa.

Kolmani
Rijiyar Kolmani Hoto: @BashirAhmaad
Asali: UGC

A lokacin da Gombawa suka yi watsi da yankin, Lauyan yace manyan jihar Bauchi sun dage wajen kai ziyara bini-bini domin suyi da’awar mallakar man.

Har ila yau, Lauyan yace a zabukan da aka rika yi a shekarun baya, wannan wuri ya fada karkashin rumfunan Bauchi, sai a yanzu magana ta fara canzawa.

“Rijiyoyi biyar da aka samu a wajen guda hudu duk a Gombe suke, daya suke cewa ta su ce ta Bauchi.
Kuma nan ma da aka duba ba jihar Bauchi ba ce, Gombe ce domin tazarar iyakar da rijiyar take da shi da iyakar Bauchi kilimota 2.50 ne.”

Kara karanta wannan

Ka gwada idan ba ga tsoro ba: Ganduje ya tsokano Kwankwaso, ya ce Tinubu ya fi shi sanuwa a Kano

- BashirAhmaad

Hukuma tace kasar Gombe ce - Lauya

Idan maganar Lauyan ta tabbata, hukumar da ke shata kan iyaka a Najeriya ta tabbatar da cewa wannan yanki yana karkashin garin Tai a Gombe.

Muddin gwamnatin jihar Gombe ba ta sa baki ba, masanin shari’ar yace zai yi kara a kotu.

Wike ya fasa kwai

A makon jiya aka samu labari Gwamna Nyesom Wike ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta biya jihohin Neja-Delta bashin kason rarar mai.

Akwai kason 13% da ake warewa Jihohin masu arzikin fetur, wanda Gwamnoni suke bin gwamnatin tarayya, Muhammadu Buhari ya biya wadannan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel