Tun Yanzu, Ana Fada Tsakanin Bauchi da Gombe a Kan Fetur da Aka Gano a Arewa

Tun Yanzu, Ana Fada Tsakanin Bauchi da Gombe a Kan Fetur da Aka Gano a Arewa

  • Mutanen Gombe da na Bauchi duk suna ikirarin su ne suka mallaki rijiyoyin man da ke Kolmani
  • Wani mai ba Gwamnan jihar Gombe shawara yace babu abin da ya hada rijiyoyin da jihar Bauchi
  • Ana zargin NNPC ce ta nunawa Gwamnatin tarayya cewa yankin da aka gano man yana Bauchi ne

Nigeria - Akwai alamun rashin jituwa a game da mallakar rijiyoyin mai da gas na Kolmani wanda gwamnati ta gano a bangaren Arewa maso gabas.

Wani dogon rahoto na Punch ya nuna cewa jami’ai da mazauna jihohin Bauchi da Gombe suna ikirarin sune suka mallaki rijiyoyin man da aka gano.

Maii ba Gwamnan Gombe shawara a kan kula da dabarun yada labaraim Alhaji Ahmed Gara-Gombe, ya yi ikirarin jiharsa ce ta mallaki Kolmani.

Kara karanta wannan

Da Dumi-duminsa: PDP Ta Yi Babban Rashi Na Sakatarenta A Wata Jihar Arewa

Ahmed Gara-Gombe ya zargi hukumar shata iyakoki da kawo sabanin da aka samu, yace rijiyoyin man da aka gano a Gombe suke ba a Bauchi ba.

Akwai laifin NNPC

Hadimin Gwamnan yake cewa NNPC ta kafa dakin bincike a Barambu a Bauchi, yace tun farko da an yi masu adalci, da ba za a samu wata rigima ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu mazauna jihar Gombe da aka tattauna da su, sun zargi tsohon shugaban kamfanin NNPC da taimakawa a wajen yaudarar gwamnatin Najeriya.

Gwamnoni
Gwamnonin Arewa maso gabas Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Da alama mazaunan suna ganin cewa Marigayi Maikanti Baru wanda mutumin Bauchi ne, ya nunawa gwamnatin Muhammadu Buhari Kolmani tana jiharsa.

Sabani ya shiga tsakani?

Tun a lokacin da aka kaddamar da shirin hako danyen man da ke yankin, gwamnonin jihohin sun yi alkawarin ba za a samu wani rikici a tsakaninsu ba.

Kara karanta wannan

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

SaharaReporters ta rahoto cewa wasu matasa a Gombe sun zargi Muhammadu Buhari da kokarin karbe dukiyarsu, ya mallakawa mutanen jihar Bauchi.

An ji wani Lauya mai suna Mohammed Abdullahi Inuwa yana cewa duka rijiyoyin man Kolmani 2,3,4 da na 5 da aka gano, suna cikin iyakar Gombe ne.

A komawa tarihi - 'Dan majalisa

Yusuf Mohammed Bako wanda ‘dan majalisar dokoki ne a Bauchi, ya yi wa Lauyan raddi, yace idan aka duba tarihi, rijiyoyin man suna cikin Alkaleri ne.

Hon. Yusuf Bako yace fiye da shekaru 100 da suka wuce Alkaleri da ke kasar Maimali tana cikin Bauchi ne, kuma a nan suke biyan haraji ba ga Gombe ba.

Lauya zai je kotu

Kwanakin baya an samu labari wani Lauya, Abdullahi Muhammad Tamatuwa ya fito yana cewa Gombe ta mallaki mai da ake shirin hakowa a Arewacin Najeriya.

Abdullahi Muhammad Tamatuwa yace doka ta tabbatar da rijiyoyin Kolmani sun fada ne a Gombe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Ayarin Gwamnan Arewa Yana Hanyar Zuwa Kamfe

Asali: Legit.ng

Online view pixel