Zaben Cike Gurbi: Masu Zabe Sun Kulle Jami'an INEC Kan Wani Dalili a Jos, Bayanai Sun Fito

Zaben Cike Gurbi: Masu Zabe Sun Kulle Jami'an INEC Kan Wani Dalili a Jos, Bayanai Sun Fito

  • An shiga wani irin yanayi a yankin Rock Haven da ke Jos ta Arewa kan takardun dangwala zabe da hukumar INEC ta kawo
  • Masu zabe sun ce dole jami'an hukumar ya nemo musu sauran kayan zaben ko kuma ya fada musu dalilin karancin takardun zaben
  • Masu zaben sun tsare jami'an hukumar da cewa har sai ya fadi dalilinsu na yin hakan idan ma akwai wata manufa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Masu zabe a Jos babban birnin jihar Plateau sun tsare jami'an hukumar INEC kan rashin isassun takardun dangwala hannu.

Mutanen sun fusata bayan kawo kayayyakin zaben wanda bai kai yawan masu zabe a rumfar 052 ba a Rock Haven da ke Jos ta Arewa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Mutane miliyan 4.6 za su zabi madadin Gbaja, Umahi da sauransu

An tsare jami'in hukumar INEC kan wata matsala
Masu Zabe Sun Kulle Jami'in INEC a Jos. Hoto: INEC.
Asali: Twitter

Mene ake zargin jami'an INEC?

Cikin fushi mutanen sun ce dole jami'an hukumar su nemo musu sauran kayan zaben ko kuma ya fada musu dalilin karancin takardun zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mutanen:

"Ba za ku bar nan wurin ba har sai kun kawo mana sauran takardun dangwala yatsun.
"Ko kuma dole ku fada mana ainihin dalilin da ya saka kuka kawo takardun kasa da yawan mutanen da ke rumfar.
"A wannan rumfa muna da mutane 1,276 amma sun kawo takardu 100, shin ba su san yawan mutanen rumfar ba ne."

Martanin masu zabe a Jos

Sun kara da cewa:

"Wannan da nufi suka yi don ganin sun hana mu kada kuri'a wanda hakan 'yancinmu ne."

Har ila yau, a mazabar Tudun Wada/Kabong, hukumar ta sake kawo kayan zaben kasa da yawan mutanen da ke rumfar zaben, Channels TV ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya rufe wurin ibada kan damun jama'a da kara, ya gargadi mutane kan saba dokar

CAN ta yi martani kan zaben cike gurbi

Kun ji cewa Kungiyar CAN reshen jihar Taraba ta yi martani kan jita-jitar dakatar da dan takarar jam’iyyar SDP.

Kungiyar ta ce wannan labarin ba shi da tushe bare makama inda ta ce ita ma samun labarin ta ke daga baya.

An ruwaito cewa kungiyar ta shawarci dan takarar SDP, Innocent Jabayang ya janyewa dan takarar PDP, Sadik Tafida a zaben cike gurbi da ake gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel