“Zan Dauki Mataki”, Ministar Buhari Ta Yi Wa EFCC Martani Kan Zargin Sa Hannunta a Badakalar N37bn

“Zan Dauki Mataki”, Ministar Buhari Ta Yi Wa EFCC Martani Kan Zargin Sa Hannunta a Badakalar N37bn

  • Tsohuwar ministar ma'aikatar ayyukan jin kai a zamanin mulkin Buhari, Sadiya Umar-Farouk ta nesanta kanta daga zargin badakalar naira biliyan 37
  • Hukumar EFCC ta kama wani dan kwangila James Okwete wanda ya fallasa alakarsa da ministar da yadda ya yi zambar makudan kudaden
  • Sai dai a martanin ta, Umar Farouk ta ce ita sam ba ta taba sanin wani Okwete ba, kuma bai taba yi mata aiki ba, don haka za ta dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sadiya Umar-Farouq, tsohuwar ministar ayyukan jin kai, ta nesanta kanta daga wani James Okwete, dan kwangilar da hukumar EFCC ke tuhuma kan badakalar naira biliyan 37.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta kama Okwete a wani bincike da take yi kan ma'aikatar ayyukan jin kai, inda kuma dan kwangilar ya ba da muhimman bayanai.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin tarayya ta fara rabawa talakawa N20,000

Sadiya Umar-Farouk ta yi wa EFCC martani kan badakalar N37bn
Tsohuwar ministar ayyukan jin kai, Sadiya Umar-Farouk ta ce ba ta da hannu a binciken badakalar N37bn da EFCC ke yi Hoto: @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

Kama Okwete ya zo dai dai da wani rahoto na cewar hukumar yaki da rashawar na binciken wasu ministoci uku da suka yi aiki karkashin tsohuwar gwamnatin Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai da ta ke martani kan yadda ake alakanta ta da dan kwangilar, Umar-Farouk ta ita sam ba ta taba sanin wani Okwete ba, kuma bai taba yi mata aiki ba, Vanguard ta ruwaito.

Zan dauki mataki don kare martaba ta - Sadiya Umar-Farouk

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin, tsohuwar ministar ta ce:

"Akwai rahotanni da ke yawo wadanda ke alakanta ni da wani bincike da hukumar EFCC ke yi kan wani James Okwete, mutumin da ban taba sanin sa ba.
"James Okwete bai taba yi mun aiki ba, bai kuma taba wakiltata ta kowanne fanni ba. Alakanta ni da shi wannan cin zarafi ne gare ni tare da bata mun suna."

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi bikin Kirsimeti ba tare da albashin Disamba ba

Yayin da Umar-Farouk ta ce ba za ta yi magana da 'yan jarida kan wannan lamarin ba, ta ce ta tuntubi tawagar lauyoyinta don daukar mataki kan wannan batanci da aka yi mata.

"Ina alfahari da aikin da na yi wa kasata matsayin minista, kuma ba zan yi kasa a guiwa ba wajen kare martaba ta da dukkan ayyukan da na yi ko a gaban waye."

A cewar tsohuwar ministar.

EFCC ta fara binciken badakalar N37bn a ma'aikatar tsohuwar ministar Buhari

A wani labarin, da yiwuwar hukumar EFCC ta kama tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk da wasu tsaffin daraktoci, biyo bayan alakanta su da wata badakalar kwangila.

Badakalar da ta rutsa da ministar jin kai da kawar da fatara ta shafi sama da naira biliyan 37 da ake zargin an yi sama da fadi da ita a gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel