Ministar da Aka Dakatar, Betta Edu Ta Shiga Hannun Hukumar EFCC

Ministar da Aka Dakatar, Betta Edu Ta Shiga Hannun Hukumar EFCC

  • Ba tare da wani bata lokaci ba, Dr. Betta Edu ta burma hannun hukumar EFCC domin amsa tambayoyi
  • Edu ta zama ministar farko da Shugaba Bola Tinubu ya dakatar tun da ya rantsar da majalisar FEC
  • A watan Agustan 2023 tsohuwar kwamishinar ta shiga ofis, ba ta wuce watanni 5 a kujerar minista ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Betta Edu wanda aka dakatar daga matsayin Ministar jin-kai da yaki da talauci a Najeriya ta na hannun EFCC.

Rahotanni daga aka samu daga jaridu irinsu Daily Trust sun tabbatar da cewa Dr. Betta Edu ta na ofishin EFCC yanzu haka.

Hukumar EFCC
Betta Edu ta je Hedikwatar Hukumar EFCC Hoto: @Edu_Betta @EFCC
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata

Hakan yana zuwa ne bayan hukumar yaki da rashin gaskiyar ta bukaci zama da Betta Edu domin yi mata wasu tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kadan bayan dakatar da ita da aka yi, sai aka ji ana neman ministar tarayyar.

Wani jami’in hukumar ya tabbatarwa jaridar an dakatar da Edu ne saboda a ji dadin binciken zargin karkatar da N585m.

An hana Edu ganin Shugaban kasa

Edu ta yi kokarin zama da shugaban kasa a ranar Litinin, amma an ji labari cewa ba a ba ta damar ganin Bola Tinubu ba.

A karshe tsohuwar kwamishinar haka ta fice daga Aso Rock Villa ba tare da ta iya yin ido biyu da Mai girma shugaban kasa ba.

Wani rahoton na Punch da aka fitar a yau Talata, ya tabbatar da Edu ta kai kan ta ofishin hukumar da ke Jabi a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Tunji Ojo: Gwamnati ta shiga binciken Ministanta da ake zargi a badakalar kwangila

Betta Edu: Masani ya ce a soke ma'aikatar

Mohammed Alhaji wanda masanin kiwon lafiya ne, ya fadawa Legit cewa kyau a soke ma’aikatar jin kai a gwamnatin tarayya.

Dr. Alhaji ya ce ko wanene yake rike da shugabancin ma’aikatar jin-kai, za ayi ta samun zargin rashin gaskiya saboda tsarin aikin.

Masanin ya nuna salon da aka bi wajen kawo tsare-tsaren tallafi ba su bada dama ayi bincike da kyau kan inda kudin su ka shiga ba

A maimakon haka, Alhaji ya ce zai fi acewa a karkatar da kudin ma’aikatar zuwa ga NPHCDA domin kula da masu rashin lafiya.

Hukumar NPHCDA ce ke dawainiya da dakunan shan magungunan da talaka yake bukata.

An saki Sadiya, an cafke Betta Edu

Kun ji cewa za binciki yadda ma’aikatarta ta raba kudi zuwa ga wasu kungiyoyi a jihohin Akwa Ibom, Legas, Kuros Riba da Ogun.

Inda ake zargin an saba ka’idar shi ne cikin asusun wani mutumi aka jefa wadannan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel