'Dan APC Ya Nemi EFCC Ta Cafke Emefiele da Wasu Ministocin Buhari Nan da Kwana 14

'Dan APC Ya Nemi EFCC Ta Cafke Emefiele da Wasu Ministocin Buhari Nan da Kwana 14

  • Dr. Haruna Garus Gololo ya na ganin akwai bukatar EFCC ta binciki wasu jami’an gwamnatin baya
  • ‘Dan siyasar ya yi Allah-wadai da abin kunyan da Hadi Sirika ya jawo a kokarin kafa jirgin Nigeria Air
  • Jigon na APC ya na Hukuma ta yi bincike a kan Godwin Emefiele da Timipre Sylva mai takarar Gwamna

Bauchi - Dr. Haruna Garus Gololo wanda yana cikin manyan jam’iyyar APC a jihar Bauchi, ya na so a binciki wasu jami’an gwamnati na kasar nan.

Jaridar The Nation ta rahoto Dr. Haruna Garus Gololo ya na cewa ya kammala shirin tursasawa hukumar EFCC yin bincike a kan Sanata Hadi Sirika.

‘Dan siyasar yana so a gurfanar da tsohon Ministan harkokin jiragen saman, kuma a hukunta shi a dalilin badakalar da aka yi ta kamfanin Nigeria Air.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

Buhari
Hadi Sirika tare da Muhammadu Buhari Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Haruna Gololo wanda yana cikin shugabannin kungiyar magoya-bayan Tinubu/Shettima a 2023 ya fadi haka da ya zanta da ‘yan jarida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jigon na APC yake cewa binciken da majalisar dattawa ta gudanar a ranar Talata, ya nuna yadda Hadi Sirika ya kashe biliyoyi, ya yaudari al’umma.

Lambar Emefiele da Sylva sun fito

Baya ga tsohon Ministan, Gololo ya nemi EFCC ta binciki Godwin Emefiele da Timipre Sylva.

"Mu na ba EFCC tsawon makonni biyu ta cafke tsohon Ministan jirage, Hadi Sirika, gwamnan CBN Godwin Emefiele da Ministan fetur, Timipre Sylva.
Haka zalika a cafke wasu manyan da aka dama da su a mulkin Muhammadu Buhari, a hukunta su.

- Dr. Haruna Garus Gololo

Gwamnan CBN da Ministan fetur

Dr. Gololo ya na mamakin yadda Timipre Sylva yake takarar Gwamna alhali shi ya bada kwangilolin fetur a lokacin yana karamin Ministan mai.

Kara karanta wannan

Ba Halin Musulmi Bane: CAN Ta Soki El-Rufai Kan Kalamansa, Ta Ce Maganarsa Ba Ta da Alaka da Musulmai

A cewar masoyin na Tinubu, Sylva ya na so ya sake zama Gwamnna ne ta yadda zai samu kariya daga doka, hakan zai ba shi dama a gagara kai shi kotu.

Da yake maganar Emefiele, Gololo ya ce dole ya yi bayani kan canjin kudi da ya kawo.

Akwai ma’aikatu da hukumomin gwamnati barkatai da aka tafka sata a mulkin APC, Gololo ya zargi Buhari da cewa sam bai san inda aka dosa ba.

Tinubu yana tare da Akpabio

A makon nan aka samu labari Muhammad Ali Ndume ya ce Bola Tinubu yana tare da Sanatan Arewa maso yammacin Akwa Ibom a zaben majalisa.

Sanata Muhammad Ndume yake cewa su na da Sanatoci 75, su ne kan gaba. Kuma su na da goyon jam’iyya, ga shugaban kasa ya mara masu baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel