Duk da Suka Daga 'Yan Arewa Ministan Tinubu Ya Dage Kan Mayar da FAAN Zuwa Legas, Ya Fadi Dalili

Duk da Suka Daga 'Yan Arewa Ministan Tinubu Ya Dage Kan Mayar da FAAN Zuwa Legas, Ya Fadi Dalili

  • Ana ci gaba da tafka muhawara kan batun mayar wasu manyan ofisoshin CBN da sauran hukumomi daga Abuja zuwa Legas
  • Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, a wata hira da aka ya da shi a baya-bayan nan, ya bayyana alfanun da ke tattare da yin hakan
  • Keyamo ya dage cewa shi ne ya ɗauki matakin ba wai Shugaba Tinubu ba kamar yadda ake hasashe a wasu ɓangarori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya dage kan mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Ministan wanda ya kasance baƙo a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels tv a yau Laraba, 31 ga watan Janairu, yace babu gudu babu ja da baya.

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya katse ziyarar da yake a Paris ya dawo gida, an bayyana dalili

Keyamo ya ce ba gudu ba ja da baya kan mayar da FAAN zuwa Legas
Keyamo ya yi nuni da gwamnati za ta rage kashe N500m idan aka mayar da FAAN zuwa Legas Hoto: Festus Keyamo
Asali: Facebook

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba gudu ba ja da baya. An ba da umarnin."

Hakan ya biyo bayan sukar da Sanata Ali Ndume, ƙungiyar dattawan Arewa (NEF) da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF), suka yi kan matakin, inda suka ce yunƙuri ne na mayar da Arewacin Najeriya saniyar ware.

Ndume ya ce akwai illar da hakan zai haifar a siyasance idan har Shugaba Tinubu ya ci gaba da aiwatar da shirin.

Sai dai a ranar Laraba, Keyamo ya ce mayar da hedikwatar hukumar ta FAAN ya zama dole duba da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.

Keyamo ya bayyana amfanin mayar da FAAN zuwa Legas

Keyamo, ya ce mayar da hedikwatar FAAN zai sanya gwamnati da al’ummar Najeriya su samu rarar rabin Naira biliyan ɗaya da jami’an hukumar suke kashewa kan tikitin jirgin da sai sun taso daga Legas zuwa Abuja su koma.

Kara karanta wannan

Duk da 'yarsa na aiki a CBN, sanatan APC ya caccaki mayar da FAAN, CBN zuwa Legas

Ya ce matakin zai taimaka wa hukumar ta samu rarar sama da Naira miliyan 500 a tafiye-tafiye kaɗai.

Akan ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sane da matakin ko bai sani ba, sai ya kada baki ya ce:

"Ni na ɗauki matakin, mataki ne da ke a ƙarƙashin kulawar minista."

Jigon PDP Ya Magantu Kan Mayar da CBN, FAAN Zuwa Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa Reno Omokri ya bayyana cewa mayar da wasu ofisoshin CBN da hedikwatar hukumar FAAN ba zai cutar da Arewacin Najeriya ba.

Jigon na jam'iyyar PDP ya yi nuni da cewa an ɗauki matakin ne domin ci gaban tattalin arziƙin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel