Yadda Amintaccen Minista Ya Yaudari Buhari Ana Saura Awanni Tinubu Ya Karbi Mulki

Yadda Amintaccen Minista Ya Yaudari Buhari Ana Saura Awanni Tinubu Ya Karbi Mulki

  • An zargi Hadi Sirika da cin amana wajen kokarin ganin gwamnati ta kafa kamfanin jirgin sama
  • Mutane sun yi surutu a kan yadda aka nemi a kawo Nigeria Air a lokacin Muhammadu Buhari
  • Wasu su na ganin Hadi Sirika wanda ya na da kusanci da shugaban Najeriya ne ya yi yadda yake so

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bayanai sun fito game da yadda Hadi Sirika ya yaudari Muhammadu Buhari da mutanen Najeriya a game da shirin kafa kamfanin Nigeria Air.

Rahoton da Vanguard ta fitar a ranar Litinin, ya nuna cewa Sanata Hadi Sirika ya yi wa gwamnatin baya dodo-rido a daidai lokacin da wa’adinsu zai kare.

Wata majiya ta shaida cewa Ministan harkokin jiragen sama a lokacin, ya nunawa shugaban kasa zai kaddamar da kamfanin jirgin Nigeria Air na kasa.

Kara karanta wannan

'Rashin Da'a Ga Buhari': Tajudeen Abbas Ya Barranta Kansa Da Kalaman Hadiminsa

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images/Samuel Alabi
Asali: Getty Images

Jirgi zai tashi babu lasisi?

Sai dai abin da Sirika bai sanar da shugaba Muhammadu Buhari ba shi ne ba a samu lasisi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana zargin tsohon Ministan ya hana jirgin saman Nigerian Eagle samun lasisin tashi a Najeriya saboda ya yi kamanceceniya da Nigeria Air da za a kafa.

Sanata Sirika ya yi yunkurin amfani da takardar shaida (AOC) na kamfanin Nigeria Air wajen kafa kamfanin jirgin saman gwamnati, amma bai dace ba.

Duk da magana ta na kotu, jaridar ta zargi Ministan (a lokacin) da nemo aron jirgin kamfanin Ethiopian Airlines, aka shigo da shi bayan ya sha fenti.

A haka aka shigo da wannan jirgi na aro ba tare da hukumar NCAA ta ba shi takardun aiki ba. Wannan lamari ya jawowa gwamnatin baya suka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

Akwai bukatar a binciki Nigeria Air

Masu ruwa da tsaki sun nuna ya kamata ayi bincike na musamman a kan sha’anin Nigeria Air

Olumide Ohunayo wanda masani ne a harkar jirage, ya zargi majalisar FEC da ta shude da amincewa da duk wasu takardu da Sirika ya gabatar mata.

Mista Ohunayo ya fadawa jaridar cewa ya kamata ayi bincike domin tun farko bai kamata majalisar zartarwar kasar ta amince da wannan kwangila ba.

A kama Sirika - Kungiya

Kwanaki an samu labari cewa wasu sun ba Hukumar EFCC tsawon makonni biyu ta cafke Ministan jiragen sama a gwamnatin da ta gabata, Hadi Sirika.

Daga baya Sirika ya maida martani ga masu caccakarsa saboda ya dauko jirgi da ke dauke da tambarin Nigeria Air da aka nemo aronsa daga kasar ketare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel