Dasuki: Na fi karfin in yi fada da wani, abin da ya faru lamarin Ubangiji ne
A Ranar Laraba, tsohon Mai bada shawara a kan harkar tsaro a Najeriya, Kanal Sambo Dasuki, ya bayyana cewa babu wani rikici da ya shiga ysakaninsa da shugaban kasa.
Duk da cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ki bada belinsa kamar yadda kotu ta bukata, Sambo Dasuki mai ritaya ya fadawa ‘Yan jarida cewa ba su da sabani.
Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya shaidawa gidan rediyon VOA Hausa na Amurka wannan ne a lokacin da su ka yi hira da shi. A jiya Talata ne aka bada umarnin sakin Dasuki.
“Ba na rikici da kowa. Na fi karfin haka. Ba zan iya rigima da kowa ba.” Kanal Dasuki ya bayyana haka a tattaunawar da aka yi da shi dazu a Ranar 25 ga Watan Disamba, 2019.
Dasuki ya godewa wadanda su ka dage da addu’o’i har aka sake shi, bayan shekaru hudu ya na tsare. Haka zalika Dasuki ya shaidawa Duniya cewa ba ya fama da rashin lafiya.
KU KARANTA: Abin da ya sa Gwamnatin Shugaba Buhari ta fito da Sambo Dasuki
“Ba ni da kalaman da zan iya amfani da su wajen yi wa ‘Yan Najeriya godiya da irin addu’o’in da su ka yi mani. Sai dai kurum ince nagode, Allah ya saka masu da alheri.”
A game da batun shari’ar da gwamnatike yi da shi na badakalar kudin makamai, Dasuki ya ce:
“Na daina zuwa kotu ne saboda an bada beli na amma gwamnati ta ki saki nam na fada duk lokacin da aka bada beli, zan hallara gaban kuliya, in kare kai na. A shirya na ke.”
Tsohon Sojan ya nuna cewa bai da labarin cewa Buhari ya garkame shi ne domin ramuwar gayya a dalilin abin da ya yi masa a lokacin juyin mulki, ya ce komai daga Allah ne.
Duk wanda ya je Masallaci a Ranar Juma’a, zai ji Limamin ya na cewa a rika yin adalci da gaskiya. Akwai dalili. A saurari wannan magana. Inji Kanal Sambo Dasuki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng