Badakala: EFCC ta gabatar da karin shaidu a kan wasu tsofin gwamnonin PDP biyu daga arewa
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kara mika shaidu uku akan shari'ar Ambasada Bashir Yuguda; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Shinkafi; Aminu Nahuche da Ibrahim Mallaha gaban Jastis Fatima Aminj ta babbar kotun tarayya dake Gusau.
Hukumar ta gurfanar da su hudun ne sakamakon zarginsu da ake da karbar kudi har naira miliyan dari hudu daga tsohuwar ministar man fetur, Deizani Allison-Madueke, saboda zaben 2015.
A takardar da shugaban yada labarai na EFCC ya bayyana a ranar Alhamis, Wilson Uwujaren, ya ce, shaidar masu kara ta biyu shine Salihu Hussein, manajan wani banki, reshen jihar Gusau, wanda ya jagoranci lauyan masu kara, Musa Isah.
A shaidarsa, Hussein ya bayyanawa kotu yadda motar daukar kudi ta kai naira miliyan dari hudu da hamsin gidan Ambasada Bashi Yuguda a ranar 27 ga watan Maris, 2015 kamar yadda hedkwatar bankin wani banki ta umarta.
Shaidar ya bayyanawa kotu cewa, bashi da masaniyar cewa kudin na da alaka da ministar man fetur.
Shaidar ya kara da cewa, Aminu Ahmed Nahuche da Ibrahim Mallaha sun he bankin don yi masa bayani kafin ya bada izinin fita da kudin.
Ya bayyana cewa, tsohon gwamna shinkafi bai he bankin ba kuma ba shi aka kaiwa kudin ba.
DUBA WANNAN: Daukaka kara: Manyan alkalai 7 da muke so su saurari shari'ar Atiku da Buhari
Shaida na uku kuwa shine sakataren jam'iyyar PDP na jihar Zamfara, Ibrahim Umar Dangaladima wanda ya bayyanawa kotun yadda aka yi kasafin kudin tsakanin kananan hukumomin jihar.
Shaida ta hudu kuwa shine Mohammed Abul Mustapha, shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Gusau.
Kafin kotun ta daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, alkalin kotun, Jastis Aminu, ya bawa tsohon gwamna Yuguda damar ya kare kansa a kan zarginsa da gabatar da shaidar rashin lafiya ta bogi bayan ya ki bayyana a gaban kotun a zamanta na farko.
Da yake kare kansa ta bakin lauyansa, Yuguda ya sanar da kotun cewa an samu kuskuren ne daga wurin 'ya'yansa da suka aiko da takardun bayan sun ji labarin cewa za a iya bayar da belinsa ne kawai bisa dalilan da suka shafi lafiyarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng