Binani vs Fintiri: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan Jihar Adamawa

Binani vs Fintiri: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan Jihar Adamawa

  • A yau Laraba, 31 ga watan Janairu, 2024, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa
  • Kotun ta yi watsi da karar da Aishatu Dahiru da APC suka shigar don neman a tsige Fintiri daga kujerar gwamnan jihar
  • Mai shari'a John Okoro ya bayyana cewa ayyana Dahiru matsayin wacce ta lashe zaben jihar tun farko ya sabawa doka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kotun koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan Adamawa.

Kotun kolin, karkashin jagorancin Mai shari’a John Okoro, ta yi watsi da karar da Aishatu Dahiru, ‘yar takarar jam’iyyar APC ta shigar kan zaben jihar na 2023, TVC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

EFCC: Yadda aka cinye Naira Biliyan 4.6 wajen yi wa Najeriya ‘addu’a’ zamanin Jonathan

Adamawa: Kotun koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri.
Adamawa: Kotun koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri. Hoto: @GovernorAUF
Asali: Twitter

Mai shari’a Okoro ya bayyana cewa ayyana Dahiru a matsayin wacce ta lashe zaben da kwamishinan zabe na jihar (REC) ya yi ya sabawa doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce jami’in zabe (RO) ne kawai dokar zabe ta ba shi ikon bayyana sakamakon zaben, kuma duk wanda ya yi hakan ya sabawa doka, rahoton Leadership.

Bugu da kari, Mai shari’a Okoro ya bayyana cewa Dahiru da APC sun kasa bayar da sahihiyar shaida da ke nuna rashin bin dokokin da suka dace ko kuma tabbatar da cewa Dahiru ta lashe zaben da kuri’u masu rinjaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel