2023: Ɗan Attahiru Bafarawa Ya Fito Takarar Gwamna a Sokoto

2023: Ɗan Attahiru Bafarawa Ya Fito Takarar Gwamna a Sokoto

  • Kwamishinan Muhalli na Jihar Sokoto, Sagir Bafarawa ya ayyana niyyarsa na fitowa takarar gwamnan jihar a zaben 2023
  • Sagir, dan tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya bayyana hakan ne a yau Alhamis bayan tuntubar shugabannin jam'iyya
  • Shugabannin PDP na Sokoto sun saka masa albarka tare da bashi goyon baya, inda ya ce zai dora daga inda Tambuwal ya tsaya idan an zabe shi

Jihar Sokoto - Sagir Bafarawa, Kwamishinan Muhalli na Jihar Sokoto, ya ayyana sha'awarsa na shiga jerin masu takarar gwamnan Sokoto a karkashin jam'iyyar PDP, rahoton TVC News.

Ita ma Daily Nigerian ta rahoto cewa, Sagir, dan tsohon gwamnan jihar, Attahiru Bafarawa, ya ayyana fitowar takararsa ne bayan taro da shugabannin jam'iyyar PDP a Sokoto, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan

2023: Ɗan Attahiru Bafarawa Ya Fito Takarar Gwamna a Sokoto.
2023: Ɗan ABafarawa Ya Fito Takarar Gwamna a Jihar Sokoto. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

Sai da na tuntubi shugabannin jam'iyya kafin na fito takara, Sagir Bafarawa

A cewarsa, ya fito takarar ne bayan kiraye-kiraye daga magoya bayansa, amma a matsayinsa na mai biyaya ga jam'iyya dole ya tattauna da shugabannin jam'iyyar kafin fitowa takarar.

"Jam'iyya tana gaba da kowa don haka ya zama dole in gana da shugabannin jam'iyya domin samun albarkarsu.
"Amma, shugabannin jam'iyyar sun goyi bayan takara ta, don haka na ke tabbatarwa mutane cewa, da izinin Allah zan yi nasara, zan dora daga inda Gwamna Aminu Tambuwal ya tsaya.
"A matsayi na na kwamishina a wannan gwamnatin,na koyi abubuwa da dama daga Gwamna Tambuwal.
"Don haka, zan cigaba daga inda ya tsaya idan an zabe ni gwamnan Jihar Sokoto," in ji shi.

Mr Sagir ya kuma yi alkawarin cewa zai cigaba da mulki mai kyau da ba zai bar kowa ba a gefe.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Jiga-jigan sanatocin APC za su gana da shugaba Buhari a yau Alhamis

Abin da shugaban PDP na Sokoto, Goronyo, ya ce game da takarar

A martaninsa, Shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Sokoto, Bello Goronyo, ya yabawa Sagir kasancewarsa mutum na farko da ya tuntubi shugabannin jam'iyyar.

"Wannan abun alheri ne ga jam'iyya, don haka muna masa fatan alheri kuma mun bashi goyon bayan mu ya fito takarar," in ji shi.

'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A bangare guda, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel