Babban Minista Ya Fadi Abu 1 da Yake Hana Shugaba Tinubu Barci

Babban Minista Ya Fadi Abu 1 da Yake Hana Shugaba Tinubu Barci

  • David Umahi, ministan ayyuka, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu yana kwana ba barci saboda halin da ƙasar nan ke ciki
  • Ministan ya yi nuni da cewa ababen more rayuwa da tattalin arziki su ne muhimman batutuwan da shugaban ya ke bakin ƙoƙarinsa wajen magance su
  • Umahi, wanda ya je garin Aba a jihar Abia domin duba wani aiki ya buƙaci ƴan Najeriya da su kasance cikin tsari a kowane lokaci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - David Umahi, ministan ayyuka, ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu yana kwana ba barci kan yadda zai warware matsalar tattalin arziƙin da ya gada.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, Umahi ya bayyana haka ne a lokacin da ya duba wani aiki a Aba a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya yi magana kan yiwuwar Kwankwaso ya koma jam'iyyar APC su sake haɗuwa

Shugaba Tinubu ba ya barci
Shugaba Tinubu na kwana ba barci kan matsalar tattalin arziki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Umahi ya ce bai dace wasu su lalata ababen more rayuwa na al’umma ba domin biyan buƙatunsu na son rai, yayin da Shugaba Tinubu ya ke fama da rashin barci kan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce:

"Yayin da shugaban ƙasa ke kwana babu barci kan yadda za a magance matsalolin tattalin arzikin da aka gada, ya kamata ƴan Najeriya su mara masa baya su kuma tallafa wa kansu."

Ɗora buri kan Shugaba Tinubu

A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya shawarci ƴan Najeriya kan kuskuren da su ka yi a baya.

Garba ya ce babban kuskuren da ƴan Najeriya suka yi shi ne ɗaurawa Buhari buri kan sauyawar komai lokaci ɗaya.

Ya roƙi ƴan Najeriya da kada su maimaita kuskuren ga gwamnatin Shugaba Tinubu kan tsammanin samun komai a gwamnatin.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya aike da muhimmin sako ga Wike da Tinubu bayan nasara a Kotun Koli

Batun Mayar da Manyan Ofisoshi Zuwa Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya yi magana kan shirin mayar da wasu manyan hukumomi da cibiyoyin gwamnati zuwa Legas.

Shettima ya bayyana cewa ko kaɗan gwamnatin tarayya ba ta da shirin aiwatar da wannan batun da ake ta jita-jita a kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel