"Taku Ta Ƙare" An Kama Ƙasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Addabi Mutanen Abuja

"Taku Ta Ƙare" An Kama Ƙasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Addabi Mutanen Abuja

  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Chinaza Phillip bayan musayar wuta
  • Rahoto ya nuna dakarun ƴan sanda sun yi gumurzu da mayaƙan Phillip kafin daga bisa su yi nasarar kama shi da kubutar da wani mutum ɗaya
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce sun yi nasarar cafke wasu imfomomi da ke taimakawa masu garkuwa a birnin tarayya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke wani mai suna Chinaza Phillip da ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Phillip a Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kano tare da masu taimaka masa da wanda suka sace, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya ɓarke bayan Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan arewa

Sufetan yan sanda na kasa.
Yan sanda sun kama kasurgumin dan garkuwa da mutane a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

An yi musayar wuta mai zafi tsakanin mutanen Phillip da ‘yan sanda, inda daga bisani aka ceto Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja da aka yi garkuwa da shi yayin da ya fito daga gidansa ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu garkuwan na kan hanyar ɗauke Akinyemi daga Abuja su maida shi Kano ne sai ƴan sanda suka tare su, in ji kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan.

Hassan ya bayyana cewa bayan samun kiran gaggawa, dakarun ƴan sanda na hedkwatar Kawo a Kaduna, suka ɗana tarko domin farautar masu garkuwan.

An kama masu yi wa ƴan bindiga leƙen asiri

A safiyar ranar Juma’a, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa an kama wasu imfomomi da ke aiki tare da masu garkuwa da mutane, rahoton Tribune.

Wike ya faɗi haka ne a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki da suka hada da mazauna garin Gwagwalada da ke karamar hukumar Gwagwalada a Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun ceto wani mutum da aka sace a Abuja, an kama mai garkuwan

Ministan, wanda ya yi magana da pidgin, ya ce:

“Shugaban kasa ya umarci in zo nan a yau. Kwanakin baya na je Bwari, haka nan a mako mai zuwa zan tafi Kwali. Tsaro daya ne daga cikin alƙawurran da Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya domin aikinsa shi ne kare rayuka da dukiyoyi.
"Idan ba za mu iya kare rayuka da dukiyoyi ba, to ba mu da dalilin kasancewa cikin gwamnati. Don haka, duk waɗannan masu laifi, ku kasance a shirye, lokacin ku ya ƙare."

Rikicin kabilanci ya jawo asara a Kogi

A wani rahoton an rasa rayuka da dukiya mai dimbin yawa yayin rikicin kalibalanci ya ɓarke tsakanin mazauna kauyuka biyu a jihar Kogi.

Mamba mai wakiltar mazaɓar Ankpa 1, Honorabul Lawal ya tabbatar da lamarin tare da kira ga mahukunta su kai agajin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel