Abin da Malaman Musulunci Suka Fadawa Tinubu Ya Fito Bayan Zaman Aso Villa

Abin da Malaman Musulunci Suka Fadawa Tinubu Ya Fito Bayan Zaman Aso Villa

  • An yi zama tsakanin shugaban kasa da Majalisar shari’a ta Najeriya a kan halin da al’umma suka shiga
  • Majalisar malamai da masana addinin musuluncin sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta kawo sauki
  • Mataimakin shugaban SCSN, Bashir Aliyu Umar ya shaidawa ‘yan jarida abin da ya kai su Aso Rock Villa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar shari’a ta Najeriya watau SCSN ta jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan wasu matakan da ya dauka.

Majalisar ta ce Mai girma shugaban kasar ya dauki wasu matakai masu daci saboda cigaban al’umma, The Cable ta kawo rahoton nan.

Tinubu
Bola Tinubu da Majalisar shari'a Hoto: @Dolusegun16
Asali: UGC

Malamai sun hadu da shugaban kasa Tinubu

Tun daga cire tallafin fetur zuwa daidaita farashin kudin kasashen waje, manyan malaman suna ganin an yi haka ne domin gyara.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sa labule da tawagar Majalisar Shari'ar Musulunci ta Najeriya a Villa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban majalisar shari’a, Dr. Bashir Aliyu Umar ya zanta da manema labarai bayan tattaunawarsu ta ranar Alhamis.

Wani ma’abocin shafin X, Muhammad El-Bonga Ibrahim ya wallafa bidiyon jawabin da Bashir Aliyu Umar ya yi a yammacin jiya.

Tinubu: Tikitin Musulmai ya biya kudin sabulu?

Shehin malamin addinin musuluncin ya ce suna jin tikitin musulmi da musulmi da aka yi amfani da shi wajen cin zabe bai biya bukata ba.

Dr. Bashir Aliyu Umar ya ce SCSN ta nemi shugaba Bola Tinubu ya gaggauta share hawayen ‘yan Najeriya da ke ciin bakar wahala.

SCSN: Abin da aka fadawa Tinubu

"Mun nemi a dauki kowane irin mataki domin rage radadin matakai masu zafi na tattalin arziki da aka dauka.
"Kuma mun bukaci ya dauko duk kayan aikin da ake da su domin magance matsalar tsaro kuma a samu abinci.

Kara karanta wannan

Daga yin kwana 7 har Tinubu ya shure umarnin da ya bada domin rage facakar kudi

"Mun zo nan yau ne saboda mu ankarar da shugaban kasa kuma mu nuna masa goyon baya da jinjinarmu kan matakan da yake dauka."

- Dr. Bashir Aliyu Umar

Majalisar ta kuma gabatarwa shugaban kasa takardar matsayar malamai, masana da kungiyoyi bayan wani taro da aka gudanar.

Dalilin zaman shi ne a ba gwamnati shawarar yadda ya kamata a shawo kan al’amura bayan babban zaben 2023 da aka yi.

Tinubu da tikitin musulmi da musulmi

Kwanai an samu labari wasu malamai kamar Sheikh Ahmad Abubakar Gumi sun ce an yaudari jama'a da tikitin APC ne a lashe zabe.

Ahmad Abubakar Gumi ya soki gwamnati ne bayan ganin take-taken Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel