Wike Ya Jawo Gumi Ya Yi Kaca-Kaca Da Gwamnati, Ya Nuna Tinubu ba Zai Zarce ba
- Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yaudarar Arewa da sunan tikitin Musulmi da Musulmi
- Shehin malamin ya yi kaca-kaca da wadanda su ka marawa APC baya ta lashe zabe, ya na mai fatan gwamnati ba za ta yi shekaru 8 ba
- A ra’ayin Dr. Ahmad Gumi birnin Abuja zai zama kamar Tel Aviv saboda sabon Minista watau Nyesom Wike zai gayyato kasar Israila
Kaduna - Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya soki Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike a game da tsare-tsaren da ya dauko.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a wani karatunsa da yake shafinsa, ya soki Nyesom Wike, har ya kira shi da shaidanin mutumi.
Shehin malamin ya zargi Ministan kasar da yunkurin hada-kai da Israila wajen kula da Abuja ta yadda za a yaki musulmai irie-irensa.
Ahmad Gumi ya na so a cire Nyesom Wike
Malamin ya tsorata da take-taken Mista Wike, ya ke cewa Abuja za ta zama tamkar birnin Tel Aviv don haka ya bukaci a cire Ministan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A faifen da yake yawo a kafafen zamani, Ahmad Gumi ya zargi manufukai da goyon bayan tikitin musulmi da musulmi da APC ta tsaida.
"Komai ya na hannun Kudu" Inji Gumi
Daily Trust ta ce malamin ya nuna duk da ma’aikatar tsaro ta na hannun mutanen Arewa ne, asalin karfin ya na ga ‘yan kudancin kasar.
Sheikh Gumi bai ambaci sunan kowa ba, amma ya nuna gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta damka duk bangaren tattali ga 'Yan Kudu.
"Ina masu tikitin musulmi-musulmi, munafukan mutane, munafukan banza? Abuja ta koma Tel-Aviv.
"Domin tsaron kasa shi ne mutane, ba ku sun yi tsit ba. Sun san abin da su ke yi. Daman take-take ne."
- Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Gwamnatin Tinubu za ta zarce har 2027?
Gumi ya ce wayau ake yi wa al’ummar Arewa, kuma gwamnati mai-ci ta na tunanin za ta yi shekaru takwas, ya na fatan ba za a zarce ba.
Tsohon sojan ya ce a tafiyar da ake yi, babu mutumin Arewa da za a bari ya ci ribar N1bn a kasuwa sai dai mai goyon bayan masu mulki.
Kiran 'Yan majalisa ga Tinubu
Ana da labari Honarabul Aliyu Sani Madakin Gini (NNPP Kano) ya kawo maganar bude iyakokin kasar nan bayan juyin mulki a Nijar.
Madaki ya ce rufe Maigatari, Kongwalam da Illela ya tsaida kasuwanci ya kawo rashin aiki yi a yankunan da ke makwabtaka da ketare.
Asali: Legit.ng