Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Cewa Bello Turji Ya Kwace Mota Mai Sulke Na Jami'ansu

Rundunar Sojin Najeriya Ta Musanta Zargin Cewa Bello Turji Ya Kwace Mota Mai Sulke Na Jami'ansu

  • Rundunar sojin Najeriya ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa Bello Turji ya kawace motar yakin rundunar
  • Daraktan hulda da jama'a na rundunar Burgediya Nwachukwu Onyema shi ya bayyana haka a yau Alhamis a Abuja
  • Ya ce faifan bidiyon da ake yadawa na bogi ne wanda an taba yada shi a ranar 9 ga watan Nuwamba na shekarar 2021

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ake cewa shugaban ‘yan bindiga Bello Turji ya kama daya daga cikin motocinsu masu sulke.

Rundunar ta mayar da martanin ne bayan wani faifan bidiyo na yawo a kafafen sadarwa cewa dan bindigan ya samu nasarar kama motar yaki na rundunar, cewar The Guardian.

Sojoji sun yi fatali da faifan bidiyon da ke cewa an kama motar yakinsu
Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Martani Kan Zargin Cewa Bello Turji Ya Kwace Motar Yakinsu. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Meye rundunar ta ce kan Bello Turji?

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hukda da jama’a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Alhamis 24 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

“Mun samu labarin wani faifan bidiyo da ake yadawa cewa kasurgumin dan bindiga Bello Turji ya kama daya daga cikin motocinmu masu sulke.
“Rundunar sojin Najeriya na son ta tabbatar wa jama’a cewa wannan ba gaskiya ba ne kuma babu abu makamancin haka da ya faru na kama motar yakinmu a Arewa maso Yammacin Najeriya.”

Wane bincike aka yi kan bidiyon?Wane bincike aka yi kan bidiyon?

Ya ce an yi kwakkwaran bincike a kan faifan bidiyon inda aka tabbatar an hada shi ne kawai don wata biyan bukata.

Ya kara da cewa:

"Binciken kwakwaf da aka yi ya tabbatar cewa an kirkiri faifan bidiyon ne.
"Dukkan motocin rundunar akwai alamar NA a jikin lambobinsu wanda kuma ba a gan shi ba a jikin motar da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Matar Aure A Bauchi Ta Kashe Jinjirin Kishiyarta

"Dadi da kari, wannan bidiyo ba a Najeriya aka dauke shi ba, an dauki faifan bidiyon ne a Burkina Faso a wani lokaci a 2021.
"An kuma tabbatar da ce akwai wadanda su ka yada bidiyon a ranar 9 ga watan Nuwamba 2021."

Onyema ya ce rundunar sojin kasar na kula da kayansu cikin kwarewa inda ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da faifan bidiyon, ThisNigeria ta tattaro,

Sojojin Sun Hallaka Aliero Da Dankarami A Wani Farmaki

A wani labarin, sojojin sama sun yi luguden wuta kan wasu 'yan bindiga tare da kashe shugabannin 'yan bindiga.

Daga cikin wadada su ka mutun akwai Ado Aliero da kuma Dankarami wadanda su ka addabi yankunan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel