Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaransa Suka Yi Garkuwa Da Su, An Bayyana Dalili 1 Da Yasa Yayi Hakan

Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaransa Suka Yi Garkuwa Da Su, An Bayyana Dalili 1 Da Yasa Yayi Hakan

  • Hatsabibin shugaban ƴan bindigan nan Bello Turji ya sako wasu mutum 20 da yaransa suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara
  • Mutanen da aka sako ɗin sun sha baƙar azaba a hannun ƴan bindigan bayan sun kwashe kwanaki 53 tsare a hannunsu
  • A cewar mutanen da aka sako ɗin, Bello Turji ya bayar da umarnin sako su ne saboda ƙoƙarin sulhu da wasu jami'an gwamnati daga Abuja suka fara

Jihar Zamfara - Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, ya sako mutum 20 da aka yi garkuwa da su da ke tsare a sansanoninsa daban-daban a yankunan Zamfara ta Arewa da sassan jihar Sokoto.

Daga cikin waɗanda aka sako ɗin akwai wata matar aure mai shekara 19 wacce aka ɗauke sati ɗaya bayan aurenta, yara ƙananan guda uku, tsaffi guda uku da wasu da aka ɗauke a gonakinsu da kan hanya.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: "Ku Ji Tsoron Allah" Manyan Malamai Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Sabbin Shugabanni

Bello Turji ya sako mutum 20 da ya yi garkuwa da su
Kasurgumin shugaban yan bindiga, Bello Turji Hoto: Tvcnews.com
Asali: UGC

An sako su ne bayan kwashe kwana 53 a hannun ƴan bindigan, inda suka riƙa kwanciya a cikin ruwa da rana sannan yaran ƴan bindigan suna azabtar da su, TVC News ta rahoto.

A cewar mutanen akwau sama da sansanonin ƴan bindiga 20 a dajin Manawa waɗanda su ke cike da ƴan bindiga masu ɗauke da miyagun makamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun bayyana cewa baƙi na zuwa kullum domin kawo musu bindigogi da alburusai da sauran kayayyaki.

Bayan sako su dai an kawo su hedikwatar 1Brigade ta sojojin Najeriya na Operation Hadarin Daji, da ke a birnin Gusau, waɗanda ke da alhakin wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

Dalilin da ya sanya Bello Turji ya sako su

Mutanen sun bayyana cewa sako su da Bello Turji ya yi, ya faru ne a dalilin wani sulhu da aka yi wanda a cewarsu an yi ne da wasu jami'ain gwamnati ne da su ke tunanin sun zo ne daga Abuja, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Rusau a Kano: 'Yan Kasuwa Sun Koma Ga Allah Sun Nemi Ya Kawo Musu Mafita Kan Halin Da Abba Ya Jefasu

Sun kuma ƙara bayyana cewa Bello Turji ya yi alƙwarin sake sako wasu mutanen nan bada daɗewa ba, saboda gwamnati ta fara tattaunawar sulhu da ƴan bindigan.

Bam Ya Tashi Da Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara

A wani labarin na daban kuma, wani bam ya tatwatsa ƙasurgumin ɗan bindigar jihar Zamfara, Dogo Gudali, wanda ya daɗe yana addabar al'ummar jihohin Arewacin Najeriya.

Dogo Gudali ya baƙunci lahira ne tare da wasu mayaƙansa bayan wasu ƴan ta'adda sun ɗana masa tarkon bam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel