Awanni Kadan Bayan Dakatar da Ita, Ministar Tinubu Ta Sha Kunya a Fadar Aso Rock, an Fadi Dalili

Awanni Kadan Bayan Dakatar da Ita, Ministar Tinubu Ta Sha Kunya a Fadar Aso Rock, an Fadi Dalili

  • Dakta Betta Edu, dakatacciyar Ministar jin kai da walwala ta gagara shiga fadar shugaban kasa a yau Litinin
  • Edu ta zo fadar shugaban kasar ce a Abuja jim kadan bayan an dakatar da ita inda ta ke neman ganawa da shugaban
  • Legit Hausa ta ji ta bakin sakataren kungiyar masu cin gajiyar N-Power ta kasa kan wannan lamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Dakatacciyar Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ta sha kunya bayan hana ta shiga wurin Tinubu.

Edu ta zo fadar shugaban kasar ce a Abuja jim kadan bayan an dakatar da ita inda ta ke neman ganawa da shugaban, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Ba kamar Buhari ba, Tinubu ya dauki mataki kan yawan kashe kudade a tafiye-tafiye, ya fadi dalili

Ministar Tinubu ta sha kunya a fadar Aso Rock a yau bayan an dakatar da ita
An hana Ministar Tinubu, Betta Edu shiga fadar shugaban kasa. Hoto: Bola Tinubu, Betta Edu.
Asali: Twitter

Mene ya faru da Minista Betta Edu?

Yayin da ta wuce dukkan shingayen jami'an tsaro, an dakatar ta ita daga ganin Shugaba Tinubu a cikin ofishinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, bayan an hana ta ganin shugaban, jami'an tsaron sun kuma kwace katin shaidar shiga fadar daga gare ta.

Daga bisani kuma jami'an tsaro sun fitar da ita daga fadar a cikin wata mota kirar Toyota Hilux ta fadar Aso Rock.

Legit Hausa ta tattauna da sakataren kungiyar masu cin gajiyar N-Power ta kasa, Kwamred Bashir Ladan.

Ladan ya ce a madadin kungiyar sun yi murna da wannan mataki da Shugaba Tinubu ya dauka.

Ya ce:

"A madadin kungiyar masu cin gajiyar N-Power ta Najeriya mun ji dadin dakatar da Minista da shugaban kasa ya yi.
"Hakan ya nuna shi mai hazaka ne kuma mai jin maganan mutane musamman matasa da suke korafi kan basukansu na watanni tara."

Kara karanta wannan

Jerin manyan mata yan siyasa 7 da aka zarga da cin hanci a Najeriya

Ya kara da cewa hana ta ganin Tinubu a fadarsa ya nuna shi mai magana daya ne wurin tabbatar da yaki da cin hanci a Najeriya.

Martanin Tinubu kan lamarin na Edu

Da ya ke martani, hadimin Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya ce an yi hakan ne don tabbatar da gaskiya kan binciken.

Ya ce:

"Wannan na daga cikin hikimar shugaban kasar don tabbatar da an yi bincike yadda ya kamata a ma'aikatar.
"Hakan shi zai ba da dama ga wadanda aka ware don marasa karfi a yi bincike don tabbatar da gaskiya."

Wannan na zuwa ne bayan zargin ta umarci Akanta Janar ta kasa ta tura mata miliyan 585 zuwa wani asusun banki na musamman.

Sadiya ta gurfana a gaban hukumar EFCC

A wani labarin, Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa tsohuwar Ministar jin kai da walwala Sadiya Farouk ta na ofishinsu.

Sadiya ta gurfana ne a gaban hukumar bayan ta ba ta wa'adin wasu lokuta ta gurfana a gabanta kan zargin badakalar kudade.

Wannan na zuwa ne bayan zargin Ministar ta wawure biliyan 37 a ma'aikatar yayin da take rike da kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel