Tashin Hankali Bayan Tirela Ta Murkushe Sabon Dan Sanda A Bakin Aiki a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

Tashin Hankali Bayan Tirela Ta Murkushe Sabon Dan Sanda A Bakin Aiki a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Wani sabon shiga aikin dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan wata babbar motar tirela ta murkushe shi har lahira
  • Mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Talata 2 ga watan Janairu a kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Ringim
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adamu ya ce bai samu rahoton lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Wani jami'in dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan babbar motar tirela ta murkushe shi a jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata 2 ga watan Janairu a kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Ringim.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

Tirela ta murkushe jami'in dan sanda har lahira a Jigawa
Tirela Ta Murkushe Sabon Dan Sanda A Bakin Aiki a Jihar Arewa. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe dan sandan ya gamu da ajalinsa?

Wata majiya ta tabbatar wa Daily Post cewa dan sandan ya gamu da ajalinsa ne yayin binciken ababan hawa a kan hanyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin mai suna Abba Safiyanu wanda aka fi sani da 'Abba Wise' sun yi kokarin tsayar da direban motar amma ya ki tsayawa.

Shaidan gani da ido, Malam Aminu ya ce direban motar ya tsere bayan murkushe jami'in dan sandan, cewar PM News.

Ya ce an kwashi jami'in dan sandan zuwa asibiti don ba shi kulawa inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Wane martani rundunar 'yan sanda ta yi?

Majiyar ta ce marigayin dan sandan na daga cikin wadanda aka diba aikin dan sanda kwanan nan inda ya ce an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adamu ya ce bai samu rahoton lamarin ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Sai dai Shiisu ya yi alkawarin bayar da bayanai da zarar ya samu labarin faruwar lamarin, Tori News ta tattaro.

Direbobin mota sun murkushe jami'an 'yan sanda 2

A wani labarin, wasu direbobin mota guda biyu sun murkushe jami'an 'yan sanda guda biyu a jihar Legas.

'Yan sandan guda biyu sun gamu da tsautsayin ne yayin da suke bakin aiki a wurin binciken ababan hawa.

An kwashe jami'an 'yan sandan zuwa asibiti bayan sun samu munanan raunaka a tare da su

Asali: Legit.ng

Online view pixel