Nazarin 2023: Kamfanonin da Suka Bar Najeriya Yayin da Ake Fama da Kallubalen Tatattalin Arziki

Nazarin 2023: Kamfanonin da Suka Bar Najeriya Yayin da Ake Fama da Kallubalen Tatattalin Arziki

  • A cikin 2023, yanayin kasuwancin Najeriya ya sha fama da kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba, masu saka jari da dama sun janye jiki daga kasar
  • Shekarar ta fara ne da karancin kudi sakamakon sake fasalin takardar kudin da aka yi, wanda ya kawo cikas ga saye da sayarwa a kasar
  • Wadannan dalilai da ma wasu, ya tilasta wasu kamfanoni dakatar da aiki a kasar, yayin da wasu suka rufe gaba daya, wasu na taka tsan-tsan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sakamakon cire tallafin man fetur da kuma hadewar kasuwar canji, kasar Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar Naira.

Wadannan matsalolin tattalin arziki, wadanda suka hada da sake fasalin naira ya haifar da ficewar kamfanoni daga Najeriya a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bankin Duniya ya lissafo jihohin da talauci, wahala da rashin tsaro za su karu a 2024

Kamfanoni 9 sun bar aiki a Najeriya
Jumia, Bolt, P&G da jerin wasu kamfanoni 6 da suka bar yin aiki a Najeriya a 2023, Legit ta yi bayanin dalilai. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ga bayanin fitattun kamfanoni da suka bar Najeriya a 2023, kamar yadda shafin Ambusinessng ya wallafa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jumia Foods:

Kamfanin manhajar wayar hannu don gano gidajen abinci da yin oda, ya fice daga Najeriya a watan Disamba.

Kamfanin ya sanar da cewa babu wata riba da ya ke samu a kasuwancin safarar dafafen abinci, don haka zai daina aiki a kasashen Africa gaba daya.

Procter & Gamble:

Kamfanin Procter & Gamble da aka fi sani da P&G ya dakatar da sarrafa kayayyakinsa a ginin kamfaninsa na Najeriya daga watan Disamba, 2023.

Sai dai kamfanin ya ce zai ci gaba da shigo da kayayyakin ne idan an hadasu a asalin kasarsa, saboda wahalar canjin kudi da faduwar darajar Naira da ta shafi gudanarwarsa.

Bolt Food:

Shi ma Bolt Food kamfani ne kamar Jumia Food da ke safarar dafaffen abinci, sai dai ya ce babu wata kasuwa a Najeriya, ga tsadar gudanar da kasuwar.

Kara karanta wannan

Mafi munin sata da rashin gaskiyar da aka yi a lokacin mulkin Buhari

Ya bar Najeriya a watan Nuwamba don alkinta jarin da ya ke kasuwancin da shi.

Equinor:

Shi kamfanin Equinor na kasa da kasa ne da ya shahara harkar man fetur da makamashi, ya bar Najeriya a watan Nuwamba.

Kamfanin ya ce matsalolin da suka mamaye masana'antar fetur a Najeriya ya tilasta shi sayar da hannun jarinsa ga kamfanin Chappal Energies don fuskantar wani abun daban.

Sanofi-Aventis Nigeria Ltd:

Wannan kamfanin Faransa ne da ya shahara a sarrafa magunguna, ya bar Najeriya a watan Nuwamba kamar dai kamfanin P&G da GSK

Amma ya ce zai ci gaba da shigo da kayansa kasar, lamarin da ya jawo asarar ayyuka da kuma hasashen tsadar kayan magunguna.

MABISCO Biscuit:

Mabisco kamfanin Najeriya ne, da ke sarrafa biskit, ya daina aiki a watan Oktoba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar da ya gurguntar da kasuwancinsu.

Kamfanin ya ce zai rufe ma'aikatarsa da ke Ogun, tare da sayar da ita don duba yiyuwar fara wani kasuwanci daban.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun katse hutu domin biyawa Bola Tinubu bukatar kasafin kudin 2024

54Gene:

Wannan kamfani ne da ya shafi magungunan kwayar halitta, ya bar aiki a watan Satumba saboda korafe-korafen ma'aikata.

Haka zalika kamfanin ya sha fama da shari'o'i duk da cewa sun yi kokarin zuba jarin dala miliyan 45 don fara kamfanin.

GlaxoSmithKline Consumer Nigeria:

Shi kuma GlaxoSmithKline kamfanin kasar Burtaniya ne wanda ke sarrafa kayan asibiti, ya bar Najeriya a watan Agusta.

Kamfanin ya ce ya bar kasar ne saboda faduwar darajar Naira, da rashin dai daiton tattalin arziki, wanda ya sa zai koma shigo da kaya kasar kawai.

Lazarpay:

Kamfanin Lazarpay ya shahara a hada-hadar kudin 'crypto' da kuma biyan kudade a yanar gizo, wani Emmanuel Njoku ne ya bude shi yana da shekaru 21 a duniya.

Ya bar aiki a Najeriya a watan Afrelu biyo bayan gaza samun hannayen jari, wanda ya tilasta rufe kamfanin bayan shekara biyu da bude shi.

Kamfanin da ke sarrafa Pampers, Oral-B, P&G ya fice daga Najeriya

Kara karanta wannan

Bikin Kirsimeti: Yan sanda sun gano bindigu an boye su cikin buhu a wata jihar Kudu

A farkon watan Disambar nan ne muka kawo maku labarin yadda kamfanin Amurka, mai sarrafa Pampers, Always, Oral B, Ariel, Ambi-pur, SafeGuard, Olay da Gillette ya dakatar da yin aiki a Najeriya.

Kamfanin ya ce rashin dai daiton tattalin arziki da yawaitar faduwar darajar Naira da wasu matsalolin ya tilasta dakatar da sarrafa kayayyakin a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.