Hukumar NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar SSCE 2023

Hukumar NECO Ta Saki Sakamakon Jarabawar SSCE 2023

  • Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) ta bana 2023
  • Hukumar ta bayyana cewa a sakamakon na bana, kaso 61.60% cikin 100 na ɗaliban da suka zana jarabawar ne suka samu kiredit biyar
  • Shugaban hukumar Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya ce an samu makarantu 93 da laifin aikata satar amsa a lokacin jarabawar

FCT, Abuja - A karshe hukumar shirya jarabawa ta ƙasa NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta 2023 wato SSCE.

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa, shugaban hukumar, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya sanar da fitar da sakamakon jarabawar a ranar Talata, 10 ga watan Oktoban 2023.

Hukumar NECO ta fitar da sakamakon SSCE 2023
Hukumar NECO ta saki sakamakon jarabawar SSCE 2023 Hoto: @olatunji_Godson
Asali: Twitter

Wushishi ya ce kaso 61.60% cikin 100 na ɗaliban da suka zauna jarabawar sun samu kiredit biyar zuwa sama waɗanda suka haɗa da Ingilishi da Lissafi.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Sama da Mutum 170 da Aka Sace a Jihar Arewa

An samu makarantun da suka yi satar amsa

Ya ƙara da cewa, an gano makarantu 93 waɗanda gaba ɗaya satar amsa suka yi, yayin aka bayar da shawarar dakatar da masu sa ido 52 saboda rashin kulawa, ba da taimako, da bada tallafi a lokacin jarabawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wushishi ya ce za a gayyaci makarantun da suka yi satar amsar zuwa hukumar domin tattaunawa, inda bayan haka za a yi musu hukuncin da ya dace.

Ya ce ɗalibai 1,196,985 da suka haɗa da maza 616,398 da mata 580,587 ne suka zana jarrabawar, ya kuma ce ɗalibai 1,543 masu bukata ta musamman ne suka zana jarabawar.

A kalamansa:

"Ɗalibai 737,308 da ke wakiltar kaso 61.60% cikin 100 ne suka yi nasarar samun kiredit biyar ko sama da haka, ɗalibai 1,013,611 masu wakiltar kaso 84.68% cikin 100 ne suka samu nasarar samun kiredit biyar ba tare da la'akari da Ingilishi da Lissafi ba."

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

Gwamnatin Bauchi Za Ta Biya Dalibai Kudi

A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Bauchi za ta riƙa biyan ɗalibai mata kuɗi domin su riƙa zuwa makaranta. Gwamnatin za ta riƙa biyan ɗalibai matan ne na makarantun sakandare.

Gwamnatin za ta riƙa biyan kuɗaɗen ne ga ɗaliban domin rage yawan yara mata da ba su zuwa makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel