Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a

Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a

- A yayin da Musulmin fadin duniya ke azumin watan Ramadan, dan majalisa Hon Abubakar Lado Suleja ya gayyaci jama'ar mazabarsa kuma ya raba musu miliyan 50

- Suleja ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa da Garara a majalisar tarayya daga jihar Neja

- Hotunan rabon kudin an wallafasu a kafar sada zumunta kuma 'yan Najeriya sun dinga tofa albarkacin bakinsu

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa da Garara ta jihar Neja a majalisar wakilai, Rt Hon Abubakar Lado Suleja, ya farantawa 'yan mazabarsa rai.

Suleja ya ziyarci mazabarsa inda ya raba kudi har naira miliyan 50 ga jama'a albarkacin wannan wata na Ramadan.

An tattaro hakan ne a wata wallafa da wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Victor Kelechi Onyendi yayi tare da hotunan rabon.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Tinubu ya gana da Buhari, yace babu shugaban kasan da zai so a gurgunta kasarsa

Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a
Dan majalisa ya gwangwaje mazabarsa da kyautar miliyan 50 na azumi, ya gigita jama'a. Hoto daga Victor Kelechi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hotunan tamfatsetsen gidan da Lionel Messi ya siya a Miami na Pam miliyan 5

Ya rubuta: "Dan majalisar wakilai na jam'iyyar APC, Rt Hon Abubakar Lado Suleja mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa da Garara ya daga mazabarsa. Ya rabawa jama'arsa naira miliyan 50 domin azumin watan Ramadan."

A yayin tsokaci, jama'a sun dinga bayyana abinda ke ransu dangane da rabon kudin nan. Wani mai suna Amb James cewa yayi hotunan sun nuna matukar soyayya.

Victor Njoku cewa yayi: "Ina yawan cewa 'yan arewa sun fi yi mana nisa a fannin hadin kai."

Uwalaka Bernard kuwa cewa yayi: "Wannan kudin da nake gani yafi miliyan hamsin fa."

A wani labari na daban, Martin Okwun, mawakin da aka fi sani da J. Martins, ya roki Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya da ya yafewa 'yan Najeriya da suka ci amanarsa tare da kiransa da miyagun sunaye yayin mulkinsa.

Mawakin yana kwatanta yanayin rashin tsaro karkashin mulkin tsohon shugaban kasan da kuma na wanda ya gaje shi, Muhammadu Buhari, a wata wallafarsa ta Instagram a ranar Talata.

Jonathan ya sha mugun kaye a kokarinsa na zarcewa mulkin kasar nan wa'adi na biyu, a hannun dan takarar jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: