An Tsare Matar da Ta Haifi ’Yan Hudu a Asibiti Saboda Gaza Biyan Naira Miliyan Hudu

An Tsare Matar da Ta Haifi ’Yan Hudu a Asibiti Saboda Gaza Biyan Naira Miliyan Hudu

  • Wani asibiti a jihar Delta ya tsare wata mata da ta haifi 'yan hudu saboda gaza biya naira miliyan hudu kudin ajiyar yaran a 'incubator'
  • Tuna watan Oktoba, 2023 matar ta haifi yaran bayan da aka yi mata aiki, kuma kullum sai sun biya naira dubu 20 duk yaro daya kudin ajiya
  • Gaza biyan kudin saboda matsalar rayuwa ya tilasta wani Comrade Agberen rubuta wasika zuwa ga al'umma don nema wa iyalin taimako

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Delta - Bayan shafe shekaru 12 babu haihuwa, Allah ya azurta wata mata a jihar Delta da samun haihuwar 'yaya hudu bayan da aka yi mata aiki a asibiti.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Jerin malamai 2 da suka hangowa kiristoci matsala a 2024

Sai dai murna ta koma ciki, yayin da asibitin kudi na Effurun suka tsare matar saboda gaza biyan naira miliyan hudu kudin aiki, magunguna da dawainiyar yaran.

Mata ta haifi 'yan hudu a Delta
An tsare matar da ta haifi ‘yan hudu a asibiti saboda gaza biyan naira miliyan hudu a Delta. Hoto: GettyImages/Diane Macdonald
Asali: Getty Images

Wani Comrade Derrick Oritsematosan Agberen ne ya fitar da sanarwar hakan mai taken "Muna neman agajin gaggawa" kuma ya raba wa manema labarai a madadin iyalan matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira miliyan hudu ta mecece?

A cewar sanarwar, matar mai suna Mrs Gladys Okodo Omodiagbe, yar asalin jihar Delta ce, mijin nata mai suna Mr Amos Omodiagbe shi ne dan asalin jihar Edo.

Wasikar ta ce an sanya yaran da aka haifa a na'urar kula da jarirai tun a ranar 21 ga watan Oktoba 2023, kuma kullum za a biya naira dubu 80 na ajiyar su, jaridar The Cable ta ruwaito.

Tribune Online ta ruwaito Agberen na rokn 'yan Najeriya da su taimaka wa matar don biyan asibiti kudin, da zai ba su damar sallamarsu su koma gida.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

Abin da sanarwar ta ce

A cikin sanarwar, Agberen ya ce:

" Matar da iyalin ta na bukatar naira miliyan hudu da naira hamsin, tuni suka biya Naira miliyan daya da rabi cikin naira miliyan biyar da rabi da aka ce su biya.
"Abin da ya sa kudin suka kai haka shi ne saboda ajiyar jariran a na'urar 'incubator', kullum kowanne yaro na cin naira dubu 20 kudin ajiya."

Asibitin sun yi iya bakin kokarin su

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Asibitin da ma'aikatansu sun iya bakin kokarin su, ba su taba nuna wa matar kyara ko wani wulakanci ba.
"Duk da cewar matar da mijin ba su iya biyan kudin ba, bai hana asibitin ci gaba da kula da 'yayan ba".

EFCC ta bukaci ministar Buhari ta mika kanta cikin ruwan sanyi

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta ce ba za ta ci gaba da daga wa tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Umar Farouk kafa ba, bayan kin amsa gayyatar da ta yi mata.

A ranar Alhamis ne Umar Farouk ta ba hukumar hakuri na cewa ba ta da lafiya ba za ta iya zuwa ofishin hukumar ba, lamarin da EFCC ta ce ba za ta sabu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel