Sadiya Umar ta kawo kanta ba tare da bata lokaci ba, EFCC

Sadiya Umar ta kawo kanta ba tare da bata lokaci ba, EFCC

  • Hukumar EFCC ta bukaci Sadiya Umar Farouk, tsohuwar ministar Buhari da ta mika kanta ga hukumar ba tare da bata lokaci ba
  • Ana zargin wani Okwete da hada baki da ma'aikatar jin kai, inda suka karkatar da akalla naira biliyan 37, lamarin da Umar Farouk ta karyata
  • EFCC ta nemi zama da tsohuwar ministar don amsa tambayoyi amma ta ki amsa gayyatar hukumar saboda 'rashin lafiya'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar yaki da rashawa (EFCC) ta bukaci Sadiya Umar Farouk, tsohuwar ministar harkokin jin kai da ta mika kanta ba tare da bata lokaci ba.

Umar Farouk ta rike mukamin minista daga shekarar 2019 zuwa 2023 a samun mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: Ministar Buhari ta bayyana babban dalilin kin amsa gayyatar EFCC, ta tura bukata 1

EFCC ta gargadi Sadiya Umar
Hukumar EFCC ta nemi Sadiya Umar Farouk ta kawo kanta ba tare da bata lokaci ba. Hoto: Sadiya Umar-Farouq, EFCC
Asali: Twitter

Shimfidar bayanai

A watan Disamba, hukumar EFCC ta cafke wani dan kwangila James Okwete bisa zargin almundahanar naira biliyan 37.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da bincike kan dan kwangilar ya kai ga alakanta satar kudin da tsohuwar ministar jin kai, Leadership ta ruwaito Sadiya tana cewa ita sam ba ta san wani Okwte ba.

A baya bayan nan ne hukumar ta gayyaci Umar Farouk don yi mata tambayoyi, amma ta ki amsar gayyatar, rahoton The Cable.

'Tana da matsalar rashin lafiyar'

A ranar Alhamis, Dele Oyewale, kakakin hukumar EFCC ya ce Umar Farouk ta sanar da masu cewar rashin lafiya ta hana ta amsa gayyatar hukumar.

A cewar Oyewale:

"Ta aiko mana da wasika tana ba da hakuri cewar ba ta da lafiya shi ya sa ba ta samu damar zuwa ba.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: Ana barazanar cafko Ministar Buhari a kan yi wa EFCC taurin kai

"Lauyan ta ya zo har ofis, ya yi mana cikakken bayani kan dalilin rashin amsa gayyatar mu.
"Matsayar hukumar shi ne dole ne Umar Farouk ta amsa wannan gayyatar ba tare da kara bata lokaci ba."

Kakakin hukumar ta EFCC ya ce ba lallai ne naira biliyan 37.1 da ake yadawa su ne gaskiyar kudin da ake zargin ma'aikatar Sadiya ta karkatar ba.

Zan dauki mataki: Sadiya Umar Farouk ta magantu kan zarginta da rashawa

A wani labarin, tsohuwar ministar jin kai, Sadiya Umar Farouk ta karyata rahoton da ake yadawa na karkatar da akalla naira biliyan 37 ta hanyar wani dan kwangila.

Hukumar EFCC ta fara kama wani dan kwangila mai suna James Okwete da laifin safarar kudin, inda ita kuma tsohuwar ministar ta ba ta taba aiki da Okwete ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.