Wata mata ta haifi 'yan hudu a Katsina (Hoto)

Wata mata ta haifi 'yan hudu a Katsina (Hoto)

Wata mata mai suna Rukayyatu Musa a garin Kayauki dake karamar hukumar Batagarawa ta jihar Katsina ta haifi yaya yan hudu ringis a jiya a asibitin mata da yara kanana ta Turai Ummaru ‘Yar’adu’a dake a cikin garin na Katsina.

Wata mata ta haifi 'yan hudu a Katsina (Hotuna)
Wata mata ta haifi 'yan hudu a Katsina (Hotuna)

Da take zantawa da majiyar mu uwar ‘ya’yan ta bayyana jin dadin ta ga yadda ta haifi yaran nata cikin koshin lafiya.

Sannan kuma tayi kira ga sauran mata a ko’ina suke da su rika zuwa awon ciki tare da bin shawarwarin malaman asibiti tun daga lokacin da suka samu juna biyu har zuwa lokacin haihuwar su.

Uwar wadda ta godewa Allah a bisa wannan babbar ni’imar da yayi mata, ta kuma ta’allaka haka da zuwan da takeyi asibiti a kan kari.

A nasu bangaren, hukumonin asibitin sun kara jan hankalin sauran iyaye mata da su rika zuwa asibiti domin duba lafiyar su data jaririn su tun daga lokacin daukar ciki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel