Binciken N37bn: Ministar Buhari Ta Bayyana Babban Dalilin Kin Amsa Gayyatar EFCC, Ta Tura Bukata 1

Binciken N37bn: Ministar Buhari Ta Bayyana Babban Dalilin Kin Amsa Gayyatar EFCC, Ta Tura Bukata 1

  • A karshe, Ministar Buhari da ake zargi da badakalar biliyan 30 ta fadi dalilin rashin amsa gayyatar hukumar EFCC
  • Sadiya Umar a cikin wata takarda da ta aike wa hukumar, ta nemi karin lokaci saboda rashin lafiya da ta ke fama da ita
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin tsohuwar Ministar da karkatar da fiye da biliyan 30 a ma'aikatar ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministar Buhari, Sadiya Umar Farouk ta bayyana dalilin kin halartar gayyatar hukumar EFCC.

Safiya ta ce ta na fama da matsanancin rashin lafiya shi ne dalilin kin mutunta gayyatar hukumar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: Ana barazanar cafko Ministar Buhari a kan yi wa EFCC taurin kai

Ministar Buhari ta bayyana dalilin rashin amsa gayyatar hukumar EFCC
Sadiya Farouk Ta Fadi Dalilin Kin Amsa Gayyatar EFCC. Sadiya Umar Farouk.
Asali: Twitter

Mene EFCC ke zargin Sadiya Farouk?

Wannan na zuwa ne bayan zargin tsohuwar Ministar da karkatar da fiye da biliyan 30 a ma'aikatar ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta tura mata takardar gayyata don amsa tambayoyi kan korafe-korafen da ake yi a kanta amma ba ta amsa gayyatar ba.

Daga bisani hukumar ta yi barazanar kame ta zuwa ofishinta don jin bahasi game da zarge-zargen da ke kanta, BusinessDay ta tattaro.

Da ya ke mai da martani, Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya ce tsohuwar ministar ta tura musu takarda inda ta bukaci karin lokaci saboda rashin lafiya.

Wane dalili Sadiya ta bai wa EFCC?

Dele ya ce:

"Tsohuwar Ministar jin kai da walwala ba ta samu amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi mata ba inda ta bayyana rashin lafiya a matsayin dalili.
"Har ila yau, ta nemi karin lokaci don samun damar zuwa ofishin hukumar bayan ta tura lauyoyinta don wakiltarta a ofishin.

Kara karanta wannan

Alumundahar N37bn: Ministan gwamnatin Buhari Sadiya Farouq ta yi biris da gayyatar EFCC

"Daga bisani hukumar ta umarce ta da ta halarci ofishin ba tare da ba ta lokaci ba, har yanzu muna kan bincike ba za mu iya sanin adadin kudaden ba."

Punch ta tattaro cewa Sadiya ba ta amsa gayyatar hukumar ba a jiya Laraba 3 ga watan Janairu har bayan awanni takwas ba tare da bayani ba.

EFCC sun yi barazanar kame tsohuwar Minista

A wani labarin, Hukumar EFCC ta yi barazanar kama tsohuwar Ministar jin kai da walwala, Sadiya Umar Farouk.

Wannan na zuwa ne bayan zarginta da karkatar da fiye da naira biliyan 30 a ma'aikatarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel