Wata amarya yar Arewa ta samu mota, da tsadaddun kayayyaki a matsayin kayan lefe

Wata amarya yar Arewa ta samu mota, da tsadaddun kayayyaki a matsayin kayan lefe

Hotuna na wata amarya yar Arewa da ta samu tarin akwatunan lefe kamar na Zahra Buhari yayi yawo a yanar gizo.

Wata amarya yar Arewa ta samu mota, da tsadaddun kayayyaki a matsayin kayan lefe
Kayan lefe

Ya kasance cikin al’addun arewa yi wa amarya akwatunnan lefe, wanda ke dauke da kayayyakin sawa, turaruka da sauran abubuwan da mace ke bukata, ya danganta da aljihun angon. Ana kiran wannan kayan al’ada dake nuna cewa angon zai iya daukar nauyin amaryansa a matsayin kayan zance.

KU KARANTA KUMA: Auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi (yanda yake wakana)

Mazan arewa na iya bakin kokarinsu gurin ganin sun burge idan aka zo kan kayan zance domin ta hakan ne zasu nuna bajinta ga yan’uwan amaryan. Wannan ango ya haura sama lokacin da ya kai wa matarsa akwatunan lefe sama da 20 da kuma mota. Kalli hoton a kasa.

Wata amarya yar Arewa ta samu mota, da tsadaddun kayayyaki a matsayin kayan lefe
Ma'auratan da kayan lefe

Ku tuna cewa a makonni da suka wuce ne aka gabatar wa Zahra Buhari akwatunnan lefe da yawa da kuma tsadaddun kyaututtuka daga angwanta Ahmed Indimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng