Ina Za Ki Damu: Mata Ta Hada Baki da Mijinta Sun Hallaka Abokinsa a Kano

Ina Za Ki Damu: Mata Ta Hada Baki da Mijinta Sun Hallaka Abokinsa a Kano

  • Ana zargin wata matar aure da mijinta da hada baki wajen kashe abokinsa a karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano
  • An rahoto cewa matar ta yi amfani da wuka wajen caccakar abokin mijin a kahon zuci da wuyansa wanda ya yi sanadiyar rasa ransa
  • Zuwa yanzu rundunar yan sandan jihar Kano bata ta fitar da bayani a kan al'amarin ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Rahotanni da ke zuwa daga yankin unguwa uku da ke karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano sun kawo cewa wata matar aure ta hada kai da mijinta inda suka kashe abokinsa.

Kamar yadda @Ussyy___ ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, daya daga cikin yan uwan mamacin mai suna Sunusi Abdullahi Gwarando ya tabbatar da faruwa lamarin.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya ta koka bayan ta bude jakar yar aiki a gida, ta ga abubuwan ban mamaki a ciki

Ana zargin mata da kashe abokin mijinta
Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A cewarsa, Gwarando ya ce tuni matar ta amsa laifinta inda ta jaddada cewar ta caka masa wuka ne a wuya da kahon zuciyarsa. Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ɗan uwana ne na jini kuma ƙani yake a gare ni.
"Ya gamu da ajalin sa ne a jihar Kano karamar hukumar Tarauni cikin unguwa uku.
"Abokin sa da matar abokin nasa, su suka shirya komai da kan su, kuma matar ta amsa yi masa kisan gilla..!
"Matar ta amsa da bakin ta ita ta caccakka masa wuka a wuya da kahon zuciya da kuma gefen cikin sa har ya mutu..!
"Yanzu haka mutum uku suna hannun jami'an tsaro mijin da matar da kuma wanda ya tattare shi ya sa likafani da sunan ya masa wanka."

Ba haka kurum ‘dana ya mutu ba, kashe min shi aka yi, Mahaifin Marigayi Nafi’u

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

Har ila yau, wani bidiyo ya bayyana a dandalin Instagram inda Malam Hafizu Gorondo, mahaifin marigayin mai suna Nafiu ya yi bayani kan rasuwar dan nasa.

Malam Hafizu wanda ke zaune a jihar Bauchi ya bayyana cewa abokin dan nasa ne ya kira shi daga jihar Kano cewa Allah ya yi masa rasuwa sakamakon aikin da aka yi masa a kwanakin baya.

Ya bayyana cewar da daddare aka sanar da su labarin mutuwar kuma ko kafin su isa garin Kano daga jihar Bauchi sun tarar an nade marigayin a cikin likafani bayan an sanar masu cewa ciwon shi ne ya tashi kuma ya yi ajalinsa.

Sai dai mahaifin yaron ya ce har ransa bai gamsu da hakan ba saboda yanayin yadda suka riski abubuwa bayan isarsu Kano.

Ya ce:

"An yi wa dana kisan gilla ne ba rashin lafiyar da ta same shi kwanakin baya ba ne sanadin.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya hana ma'aikata sanya babban riga da kaftani? Gaskiya ta bayyana

“Da farko sun yaudare ni da cewar ciwon sa ya tashi kuma Allah ya yi wa Nafiu rasuwa, sai suka tambaye ni yaushe za mu masa sallah jana’iza sai nace musa karfe 10.
"Bayan na isa Kano har karfe 7 na safe ban fahimci akwai wani abu ba sai da muka sake kallon gawa sai muka ga jini na ta zuba.
“Anan na bukaci a bude gawar sa mu gani, ina budewa sai naga kota ina a wuyan sa an caccaka masa wuka.
"Shine muka tafi wajen ‘yan sanda suka zo suka dauki hotuna da jawabai kuma sun kama wadanda ake zargi da hannu a kisan."

Sai dai kuma, zuwa yanzu ba a samu wata sanarwa daga rundunar yan sandan jihar Kano a kan wannan al'amari ba.

Matar ta amsa laifinta, inji mahaifin marigayin

Ya kuma tabbatar da cewar matar ta sanar da hukumar yan sanda cewa ita ta aikata masa wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan

Direban tasi ya tsinci jakar kudi a motarsa, bidiyo ya bayyana yayin da ya mayar da shi

A cewarsa bayan ta aikata kisan kan, ta sanar da mijinta inda shi kuma ya nemo malamin karya suka nade shi da sunan yi masa sutura. Ya kuma ce sun ga digo-digon jini a wurare da dama a gidan.

Ga bidiyon hirar da aka yi da Mahaifin marigayin a kasa:

Soja ya rasu gabannin daurin aurensa

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023, Salihu Yakasai ya yi alhinin mutuwar wani jami'in sojan Najeriya wanda ya rasu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa.

Kamar yadda dan takarar gwamnan ya bayyana a shafinsa na X, an shirya za a yi auren sojan mai suna Ya'u Yunusa a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, kafin ya hadu da ajalinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng