Ministoci 3 Sun Koka da Kasafin Kudin 2024, Abin da Tinubu Ya Ware Masu Ya Yi Kadan

Ministoci 3 Sun Koka da Kasafin Kudin 2024, Abin da Tinubu Ya Ware Masu Ya Yi Kadan

  • Babban Ministan tsaro ya roki ‘Yan majalisa su kara adadin kudin da ma’aikatarsa za ta kashe a shekarar 2024
  • Badaru Abubakar da wasu Ministoci sun ce abin da aka ware masu a kasafin kudin shekarar badi ba zai isa ba
  • Dele Alake ya roki kwamitin da ke kula da ma’aikatarsa a majalisar tarayya ya kara masa Naira biliyan 250

Abuja - Babban Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya bukaci majalisar tarayya ta kara adadin kudin ma’aikatar tsaro.

A ranar Laraba Premium Times ta rahoto Muhammad Badaru Abubakar cewa ya roki a kara kason ma’aikatarsa a cikin kasafin 2024.

Tinubu da kasafin kudi
Ministoci sun ce kasafin kudin 2024 ya yi kadan Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Ministan tsaro yace kasafin 2024 ba zai isa ba

Ministan tsaron Najeriyan ya nemi wannan alfarma ne da ya zauna da kwamitin hadaka na tsaro a majalisar tarayya a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Ministan ya nuna N78.5bn da aka ware a matsayin kudin da za a kashewa ma’aikatar tsaro a 2024 ya yi masu kadan.

Tsohon gwamnan Jigawa ya fadawa Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan cewa kudin ba za su isa a tunkari matsalar tsaro a Najeriya ba.

Ministar walwala ta kokawa Majalisa

Ministar tallafawa al’umma da yaki da talauci, Dr. Betta Edu ta yi irin wannan kuka a lokacin da ta zauna da ‘yan majalisar tarayya.

Mai girma Ministar ta ce babu abin da aka warewa gidauniyar da aka kafa domin yakar talauci, ta ce N532.5bn ya yi mata kadan.

Duk da haka, The Nation ta ce an samu karin 28% kan kasafin kudin 2023 a sakamakon tashin da kaya su ka yi yanzu a kasuwa.

Dele Alake ya nemi karin N250bn

Kara karanta wannan

Ministoci 10 da za su tashi da 86% na duka kudin da za a kashe a Najeriya a 2024

Wasu Ministocin sun roki a kara kudin ne a sakamakon tashin farashin dizil da fetur.

Dele Alake wanda shi ne Ministan harkokin ma’adanai ya roki Sanatoci da ‘Yan majalisar wakilai su sake duba kasafin ma’aikatarsa.

Premium Times ta rahoto cewa Alake yana neman karin N250bn a kasafin kudin 2024.

Ministoci a kundin kasafin 2024

Ministoci 15 za su fi morewa da kasafin kudin shekara mai zuwa da Bola Ahmed Tinubu ya kai majalisa domin nema amincewarsu.

Lissafin da mu kayi ya nuna a kasafin kudin na badi, Wale Edun, Atiku Bagudu, Badaru Abubakar da Tahir Mamman za su samu N16tr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel