Ana Cikin Halin Matsi, Babban Malamin Addini Zai Ciyar da Yara 1000

Ana Cikin Halin Matsi, Babban Malamin Addini Zai Ciyar da Yara 1000

  • Fasto Christson Orovwuje ya shirya faranta ran yara marasa galihu a jihar Delta dake yankin Kudu maso Kudu
  • Shugaban cocin na Pacesetters Prophetic Interdenominational Ministry a Warri, ya sanar da shirin ciyar da yara 1000
  • Babban faston wanda ya yi bayani kan muhimmancin hakan zai gudanar da shirin ciyar da yaran ne a watan Janairun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Warri, Delta - Fasto Christson Orovwuje na cocin Pacesetters Prophetic Interdenominational Ministry a Warri ya bayyana shirin samar da abinci ga yara sama da 1000 a cikin watan Janairun 2024.

An sanar da hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, daidai da ƙaddamar da shirin ‘God of Suddenly’ da aka shirya gudanarwa a watan Janairun 2024 a garin Warri na jihar Delta.

Kara karanta wannan

Matawalle ya yi wa sojoji muhimmin abu 1 bayan sun halaka yan bindiga 30 a Neja

Fasto Orovwuje zai ciyar da yara 1000
Fasto Orovwuje ya sanar da shirin ciyar da yara 1000 Hoto: Facebook/Getty Images
Asali: UGC

Meyasa faston zai ciyar da yara 1000?

A ƙarfafa rawar da Ikilisiya ke takawa a cikin al'umma bayan ayyukanta na ruhaniya, Fasto Orovwuje ya bayyana nauyin da ke kanta a cikin ilimi, kiwon lafiya, da ayyukan agaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Alhakin zamantakewa na Kirista (CSR) wajibi ne na tushen ban gaskiya domin saduwa da buƙatun al'umma ta hanyar nuna ƙauna wanda ke tasiri ga al'ummomi da daidaikun mutane, jaddada cewa CSR yana da tushensa a cikin Kiristanci kuma Coci yana nufin ya zama misali ga duniya, cewar Matt. 5:16"

Ya koka kan yawaitar yunwa

Da yake bayyana damuwarsa game da yawaitar yunwa da ke addabar iyalai, musamman yara, ya jaddada cewa magance matsalar yunwa muhimmin lamari ne na jin ƙai a ƙasashe masu tasowa da masu cigaba da ya kamata a kula da su baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da suka faru gabanin yan Majalisa 27 su sauya sheka daga PDP zuwa APC

"Saboda haka, dole ne mu damu sosai kuma mu yi ƙoƙarin yin abin da za mu iya domin taimakawa marasa galihu a matsayin ma’aikatar." A cewarsa.

Faston ya jaddada ƙalubalen da mutane da yawa ke fuskanta a duniya, har ma a ƙasashe masu wadata, inda samun abinci yake zama wani babban abun gwagwarmaya.

Da yake ƙarfafa gwiwar mazauna Warri su shiga cikin shirin mai zuwa, ya jaddada cewa alhakin zamantakewa na Kirista ba domin neman yabo daga wasu ba ne amma nuna ƙaunar Kristi da kuma ba da gudummawa mai kyau ga al'umma.

Fasto Mai Azumi Ya Kasa Tafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Victor Great, babban faston cocin Zion Ark of Covenant Int’l Bible Church Inc. a jihar Delta, ya kasa tafiya bayan ya kwashe kwanaki 21 yana azumi da addu'a.

An dai nuna faston ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook sanye da fararen kaya inda hadiman cocin suka ɗauke shi daga motarsa ​​zuwa bagaden cocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel