Lafiya uwar jiki: Anfanin ruwan zuma 10 a jikin dan adam da baku sani ba

Lafiya uwar jiki: Anfanin ruwan zuma 10 a jikin dan adam da baku sani ba

Zuma dai kamar yadda muka sani wata halitta ce mai matukar tasiri a rayuwar musulmai dama wadan da ba musulmai ba a dukkan fadin duniya.

Kasantuwar kudan zumar yana cin furanni da kuma wasu lokutan itatuwa daban daban, hakan ne ma kashin sa da yake fitar wa ake da yakinin yana magunguna da dama a cikin jikin dan adam.

Lafiya uwar jiki: Anfanin ruwan zuma 10 a jikin dan adam da baku sani ba
Lafiya uwar jiki: Anfanin ruwan zuma 10 a jikin dan adam da baku sani ba

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben su a 2019

Mutane dai na amfani da ruwan zumar a matsayin abinci ko magani ga cututtuka da dama.

Haka ma dai an ambaci zuma a wurare da dama a cikin alkur'ani mai girma saboda muhimmancin ta.

Ga dai wasu daga cikin anfanin ta nan 10 da muka tattaro maku:

1. Tana taimaka ma mai-mura, tari, atishawa da sauran matsalolin sanyi.

2. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.

3. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage` kiba.

4. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.

5. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.

6. Maganin gudawa ce.

7. Tana karfafa garkuwar jiki.

8. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.

9. Maganin gyambon ciki - Ulcer.

10. Tana kara kuzari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel