Babban fasto a jihar Delta ya kasa tafiya bayan kwashe kwana 21 yana azumi

Babban fasto a jihar Delta ya kasa tafiya bayan kwashe kwana 21 yana azumi

  • Babban faston cocin Zion Ark of Covenant Int’l Bible Church Inc. a jihar Delta, Victor Great, ya kasa tafiya bayan ya kwashe tsawon kwanaki 21 yana azumi da addu’a
  • A wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na cocin, an ga malamin sanye da fararen kaya inda aka ɗauke shi aka kai kan bagade
  • An nuna babban faston lokacin da hadiman cocin ke kwantar da shi a ƙasa, inda aka jiyo shi yana kalaman wa'azi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Asaba, jihar Delta - Victor Great, babban faston cocin Zion Ark of Covenant Int’l Bible Church Inc. a jihar Delta, ya kasa tafiya bayan ya kwashe kwanaki 21 yana azumi da addu'a.

An nuna malamin ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na cocin, sanye da fararen kaya inda hadiman cocin suka ɗauke shi daga motarsa ​​zuwa bagaden cocin.

Kara karanta wannan

Jerin Fastocin Da Suka Yi Hasashen Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

Tafiya ta gagari fasto bayan azumin kwana 21
Babban fasto ya kasa tafiya bayan kwashe kwana 21 yana azumi Hoto: Zion Ark of Covenant Int’l Bible Church Inc
Asali: Facebook

Sai suka kwantar da shi a hankali a ƙasa yayin da jama'a suka kewaye shi. Daga nan aka gan shi yana isar da saƙonnin wa'azi yayin da mabiyan suka mayar da hankali sosai kan saƙonnin da yake isarwa.

Me yasa fasto Victor Great ya kasa tafiya?

A ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, faston ya sanar a wani faifan bidiyo da aka saka a shafin Facebook na cocin cewa zai yi azumi 21 da addu’a don "rufe ƙofofin mutuwa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Inda zan je, ba za ku gan ni a ko’ina ba. Zan tafi wurin ɓoye, in yi kuka ga Allah saboda mutanena. An riga an buɗe ƙofar inda zan nufa. Kuna ganin wasiyyata ce? Aiki ne. Na zo nan ne domin na bijirewa ƙofar mutuwa, sannan in bayyana cewa akwai mutanen da ba za ta ɗauka ina kallo ba."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Direba Ya Cakawa Jami'in LASTMA Wuka, Ya Yi Tumbur a Bainar Jama'a

A cikin faifan bidiyon, an ji shi ya yi alkawarin tsayawa a matsayin wakilin mabiyan cocinsa a gaban ƙofar mutuwa da kuma kare duk wani mamba daga gare ta.

Fasto Elijah Ya Fadi Makomar Atiku, Obi a Kotun Koli

A wani labarin kuma, fasto Elijah Babatunde Ayodele ya bayyana cewa asarar dukoya kawai Peter Obi da Atiku Abubakar za su yi domin ɗaukaka ƙara a kotun zaɓe.

Faston ya buƙaci ƴan takarar da su yi amfani da kuɗin domin taimakon al'umma maimakon su yi asararsu a koyun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel