Ondo: Jikin Gwamna Akeredolu Ya Tsananta, Ya Mika Mulki Hannun Mataimakinsa, Ya Tafi Neman Magani

Ondo: Jikin Gwamna Akeredolu Ya Tsananta, Ya Mika Mulki Hannun Mataimakinsa, Ya Tafi Neman Magani

  • Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya mika ragamar mulkin jihar hannun mataimakinsa Richard Olatunde
  • Wannan matakin ya biyo bayan rashin lafiyar gwamnan da ta tsananta, inda ya shilla zuwa Jamus don neman magani
  • Tuni gwamnan ya aike wa majalisar dokokin jihar da takardar tafiyarsa neman magani da kuma ba Aiyedatiwa rikon jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya sanar da daukar hutu a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023 don zuwa neman lafiyarsa.

Da wannan ne Akeredolu ya mika rikon mulkin jihar hannun mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa har zuwa lokacin da zai samu cikakkiyar lafiya.

Oluwarotimi Akeredolu/ Jihar Ondo
Jikin Gwamna Akeredolu na jihar Ondo ya tsananta, ya mika mulki hannun mataimakinsa, ya tafi neman magani. Hoto: Oluwarotimi Akeredolu
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa daga babban sakataren watsa labaransa, Richard Olatunde, ya ce za a aike wa majalisar dokokin jihar takardar tafiya hutun gwamnan da mika mulki ga Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shugaba Tinubu ya umarci majalisar ta miƙa mulki ga mataimakin gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce idan gwamnan ya tafi hutun, mataimakinsa Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa, zai zama gwamnan rikon kwarya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ondo: Tinubu ya umurci majalisar jihar ta mika mulki ga Aiyedatiwa

A safiyar yau muka ruwaito maku cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dokokin jihar Ondo ta mika mulki ga mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

Wani rahoto ya nuna cewa Tinubu ya ba da umrunin ne a taron da ya kira domin magance rikicin shugabanci a Ondo a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba a Abuja

Jaridar The Nation ta rahoto cewa za a mika mulkin ne ta hanyar sanya hannu ta na'ura saboda gwamnan da ke fama da rashin lafiya ba zai iya sanya hannu kan wata takarda ba.

Gwamna Akeredolu zai yi murabus saboda rashin lafiya?

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata, ya sake saka baki a rikici tsakanin gwamnan APC da mataimakinsa, ya dauki mataki

Ko a farkon watan Disamba, sai da Legit Hausa ta ruwaito irin takaddamar da ake tafkawa a jihar Ondo, na yiwuwar gwamnan jihar ya yi murabus saboda rashin lafiyarsa.

Duk da yunkurin wasu na tilasta gwamnan yin murabus, kwamishinar yada labaran jihar, Mis Bamidele Ademola-Olateju, ta bayyana dalilin da ya sa Akeredolu ba zai yi murabus ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel