Yanzun Nan: Gobara Ta Tashi a Ofishin Gwamnan Jihar Borno

Yanzun Nan: Gobara Ta Tashi a Ofishin Gwamnan Jihar Borno

  • Gobara ta tashi a ofishin Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata, 12 ga watan Disamba
  • An rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12: 29 na ra lokacin gwamnan na daya ofishinsa a sakatariyar Musa Usman
  • Yanzu haka yan kwana-kwana sun dukufa aikin tabbatar da kashe wutan yayin da yan sanda suka hana motoci, mutane da manema labarai shiga gidan gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Birno - Rahotanni da ke zuwa sun kawo cewa gobara ta tashi a ofishin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a safiyar yau Talata, 12 ga watan Disamba.

Kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X ( wanda aka fi sani da Twitter a baya) ya ce zuwa yanzu ba a tabbatar da irin barnar da gobarar da ta kama ainahn ofishin gwamnan ta yi ba.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki yayin da wani mutum ya kashe da birne mahaifiyarsa da kanwarsa a karamin rami

Gobara ta kama ofishin gwamnan Borno
Yanzun Nan: Gobara Ta Kama Ofishin Gwamnan Jihar Borno Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Yan kwana-kwana sun kai dauki

An tattaro cewa gwamnan na a daya ofishinsa da ke sakatariyar Musa Usman lokacin da lamarin ya afku da misalin karfe 12:29 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rahoto cewa an gano motocin hukumar kwana-kwana suna fita daga gidan gwamnati a kokarinsu na kashe gobarar.

Rundunar yan sanda sun hana motoci, ma’aikata da manema labarai shiga gidan gwamnatin tun daga babban kofar shiga.

Motar mai ta fashe a Kaduna

A wani labari na daban, mun ji cewa wata babbar motar dakon mai ɗauke da man dizel ta fashe kuma ta yi filla-filla a yankin Ojota da ke jihar Legas ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023

Hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa ta jihar Legas, (LASTMA), ce ta tabbatar da aukuwar ibtila'in a shafinta na manhajar X wadda aka fi sani da Tuwita.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Hukumar ta kuma bayyana cewa tuni ta tura jami'anta zuwa wurin domin kai agajin da ya kamata da kuma shawo kan lamarin a kan lokaci.

Gobara ta lakume dukiya a Jigawa

A wani labarin kuma, mun ji cewa shaguna da kayayyaki masu daraja da kudinsa ya kai miliyoyi sun lalace a Bakin Kasuwa da ke Karamar Hukumar Hadejia na jihar Jigawa a ranar Juma'a.

Adamu Shehu, mai magana da yawun Hukumar Tsaro na NSCDC na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel