Wani Matashi Ya Fara Tattaki Akan Keke Daga Jihar Yobe Zuwa Delta, Zai Shafe Kilo Mita 1,200

Wani Matashi Ya Fara Tattaki Akan Keke Daga Jihar Yobe Zuwa Delta, Zai Shafe Kilo Mita 1,200

  • Wani mutum dan jihar Yobe ya fara wani tattaki akan keke daga Damaturu zuwa jihar Delta don ganawa da Gwamna Sheriff Oborevwori
  • Tafiyar wacce za ta shafe kilo mita 1,200 za ta iya daukar mutumin kwanaki 10 zuwa 15 kafin ya isa
  • A cewar Mr Samuel Okoro, sai da ya ziyarci asibiti aka duba laifiyarsa tare da ziyartar jami'an tsaro don neman shawarwari kafin ya fara tafiyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Yobe - Samuel Erukoghene Okoro, wani mazaunin jihar Yobe ya fara wani tattaki akan keke daga Damaturu zuwa Asaba, jihar Delta, tafiyar da za ta shafe tsawon kilo mita 1,200.

Mr Okoro, mahaifin yara biyu, wanda ya fito daga jihar Delta, ya shafe sama da shekaru takwas yana rayuwa a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

"Yan sanda sun yi garkuwa da ni, sun karbi Naira miliyan 1 kudin fansa", cewar Mr Soyemi

Dan Najeriya ya fara tattaki daga jihar Yobe zuwa jihar Delta akan keke
Wani mutum, Mr Oko ya fara tattaki akan keke daga Damaturu zuwa jihar Delta don ganawa da Gwamna Sheriff Oborevwori. Hoto: @ossaioviesuccess
Asali: Facebook

Da ya ke zantawa da City & Crime, ya ce ya kuduri wannan doguwar tafiya akan keke don nuna goyon bayansa ga Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta kan ayyukan da ya ke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mr Okoro ya yi shir tsaf kafin fara wannan tattaki

Ya ce 'yan Kudu da ke rayuwa a jihar Yobe sun ba shi wata wasika da zai kai wa gwamnan jihar idan har ya samu isa.

Mr Okoro ya bayyana cewa kafin ya fara wannan tattaki, sai dai ya ziyarci asibiti aka duba laifiyarsa don tabbatar da cewa zai iya zuwa Delta daga jihar Yobe akan keke.

Ya kuma ce jami'an tsaro sun shawarce shi da ya bi ta cikin garin Jos, jihar Filato sakamakon matsalolin tsaro da hanyar Damaturu zuwa Kano ta ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

Ya kara da cewa yana ra san wannan tafiyar ta dauke shi kwanaki 10, ko kuma tsanani zuwa kwanaki 12, kamar yadda shafin Ossai Ovie Success ya wallafa hotunansa a Facebook.

Duba hotunan a kasa:

Matafiya ayi hattara: Babbar gadar fita daga Legas ta ruguje

Wani rahotan Legit Hausa ya yi nuni da cewa babbar gadar Alapere ta rushe sakamakon wata tirela dauke da kwantena da ta hau kanta a makon da ya gabata.

Hatsarin ya faru ne a daren jiya, wanda ya shafi hannun fita daga jihar Legas da ke babbar gadar 'Mainland' ta uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel