"Cin Zabe Sai An Hada da Rauhanai" Shehu Sani Ya Yi Wa Doguwa Martani

"Cin Zabe Sai An Hada da Rauhanai" Shehu Sani Ya Yi Wa Doguwa Martani

  • Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya ce lashe zabe ba wai da yawan kuri'u bane kawai
  • Sanata Shehu Sani ya ce "aikin rauhanai ne" a lokacin da ya ke martani kan kalaman Doguwa da ya jawo cece kuce
  • Yan Najeriya a soshiyal midiya sun yi martani ga furucin Doguwa da ikirarin cewa katin zabe baya tasiri a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Tsohon dan majalisar tarayyam Shehu Sani, ya yi martani ga furucin da aka ce tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi cewa cin zabe ba wai ga yawan kuri'un da aka kada bane kawai.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda malami ya jagoranci dalibansa wajen ciccibo yaron da ke yawan fashin makaranta ya yadu

Da yake jawabi yayin wata hira a Channels TV a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, Doguwa ya ce cin zabe yana da nasaba da bin ka'idojin wasan, Daily Trust ta rahoto.

Shehu Sani ya yi martani ga Doguwa kan tsarin cin zabe
Shehu Sani Ya Yi Martani Ga Ikirarin Doguwa Na Cewa Ba Yawan Kuri’u Ke Sa a Ci Zabe Ba Hoto: Ado Doguwa/Shehu Sani
Asali: Facebook

Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga takaddamar da ke kewaye da zaben 2023 a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abun da mutanenmu suka gaza fahimta ko wasu daga cikin mutanenmu shine rashin fahimtar cewa, zabuka musamman a tsarin dimokradiyya irin wanda muke gudanarwa a Najeriya a kodayaushe ya shafi ka’idojin wasa ne, ba wai kawai na ci zabe ba ne."

Da yake martani ga furucin Doguwa a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya), @ShehuSani, a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, ya rubuta a takaice: "Ta hanyar amfani da ruhanai ne."

Kara karanta wannan

Zaben Kano: Yawan kuri'u ba shi ne kadai alamar nasara a zabe ba, cewar Doguwa

Yan Najeriya sun yi martani

@Doc_steena

"Muna sane kwarai da gaske. Ta hanyar sacewa da guduwa da shi ne da dan surkullen bangaren shari'a."

@SylverValentina

"Cin zabe ba wai ta yawan kuri'u bane kawai ta wanda ya fi sake bakin aljihu ne a kotun."

@SabinaNkiru

"Sun rasa shi gaba daya. Suna bude bakunansu suna amayar da ta'asar da suke tafkawa."

@Faithfu20237471

"Hakan na nufin cewa katin zabenmu bai da amfani."

Shehu Sani ya shawarci Dino Melaye

A wani labarin, mun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya mayar da martani ga ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a ƙarkashin jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye, kan ƙin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba.

Sani ya ce yana goyon bayan matakin Melaye na ƙin zuwa kotu bayan ya zo na uku a bayan ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Usman Ahmed Ododo da Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel