Alkalluma: Yan Najeriya Miliyan 1.8 Na Dauke da Cutar Kanjamau, Majalisar Tarayya Ta Dauki Mataki

Alkalluma: Yan Najeriya Miliyan 1.8 Na Dauke da Cutar Kanjamau, Majalisar Tarayya Ta Dauki Mataki

  • Sabuwar kididdiga ta nuna cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 1.8 ne ke rayuwa da cutar kanjamau a jikinsu
  • Sabon binciken ya kuma nuna cewa kaso 58% na masu dauke da cutar mata ne, yayin da kaso 42% suka kasance maza
  • Sai dai, majalisar dokokin Najeriya ta sa hannu a lamarin, inda ta shirya nemo kudi domin dakile cutar daga yaduwa a kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Majalisar dokokin Najeriya ta duaki mataki na tabbatar da cewa ta samar da wadatattun kudade don yaki da cutar kanjamau a Najeriya.

Shugaban kwamitin yaki da kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro na majalisar, Amobi Oga, ya sanar da hakan a Abuja, a shirin ranar cutar kanjamu ta duniya, 2023.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Masu dauke da kanjamau
Alkalluma sun nuna kaso 58% na masu dauke da kanjamau mata ne, maza kuma kaso 42% Hoto: Facebook
Asali: UGC

Ana gudanar da bikin ranar kanjamau ta duniya a ranar 1 ga watan Disamba na kowacce shekara domin wayar da kai da kuma tuna wa da wadanda cutar ka kashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taken bikin ranar kanjamau ta duniya na wannan shekarar shi ne "Al'umma: Shugabanci domin kawar da kanjamau zuwa 2030"

Oga, wanda wakili ne na mazabar Isuikwuato/Umuneochi a majalisar tarayyar, ya tabbatar da cewa za su tallafawa hukumar yaki da cutar kanjamau don dakile yaduwar ta.

Haka zalika ya yi alkawarin samar da wata doka a majalisar da za ta kare 'yancin mutane masu dauke da cutar kanjamau (PLHIV) don kare su daga tsangwamar jama'a.

Kanjamau a Najeriya: Mutane miliyan 1.63 na karbar magani - Gwamnati

Gambo Aliyu, daraktan hukumar NACA, ya ce akalla 'yan Najeriya miliyan 1.8 ke rayuwa da kanjamau, yayin da miliyan 1.63 ke karbar maganin rigakafin cutar.

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

Aliyu ya ce:

"Najeriya ce kasa ta biyu a masu dauke da cutar kanjamau. Akalla mutane miliyan 1.8 ke dauke da ita, amma mutane miliyan 1.63 na shan magani.
"Haka nan mata ke da kaso 58% yayin da maza ke da kaso 42%. Shigar cutar jikin jarirai daga iyayensu na da kaso 25, wasu jihohin ma kaso 15."

Da ya ke magana kan taken bikin ranar na wannan shekarar, Aliyu ya bayyana muhimmiyar rawar da al'umma za su taka wajen yaki da kanjamau.

Magidanci ya gane matarsa na da kanjamau bayan shekara 3 da aure

A wani labarin, wani mutumi da yayi aure shekaru uku da suka shude ya fallasa yadda matarsa ke boye masa tana dauke da cutar kanjamau, rahoton Legit Hausa.

Mutumin ya ce Ubangiji ne ya tona mata asiri yayin da yake ibada a boye gami da nuna masa inda take ajiye magungunanta na Kanjamau

Asali: Legit.ng

Online view pixel