Na Yarda da Ita: Magidanci Ya Gane Matarsa na da Kanjamau Bayan Shekara 3 da Aure

Na Yarda da Ita: Magidanci Ya Gane Matarsa na da Kanjamau Bayan Shekara 3 da Aure

  • Wani mutumi da yayi aure shekaru uku da suka shude ya fallasa yadda matarsa ke boye masa tana dauke da cutar kanjamau
  • Mutumin ya ce Ubangiji ne ya tona mata asiri yayin da yake ibada a boye gami da nuna masa inda take ajiye magungunanta na Kanjamau
  • Ya koka matuka, inda yake cewa duk irin amintar da yayi da ita da zuciya daya, amma ta zabi yaudararsa

Wani mutumi ya bayyana yadda ya gano matar da yake tare da ita tsawon shekaru uku tana dauke da cutar tsida kuma shan maganin kanjamau a boye a bidiyo. Mutumin ya shiga bayan wata kujera s falonsu, inda ya bude wani murfin da ta boye magungunan kanjamanta.

Matar Aure Mai Kanjamau
Na Yarda da Ita: Magidanci Ya Gane Matarsa na da Kanjamau Bayan Shekara 3 da Aure. Hoto daga TikTok/@ewurabena091, Rick Gomez
Asali: UGC

Game da yadda ya gano, a cewarsa Ubangiji ne ya nuna masa cikin ibadarsa.

Kara karanta wannan

Wani Magidanci, Nuhu Usman, Ya Bindige Matarsa Har Lahira A Bauchi

Yayin da yake godiya ga Ubangiji bisa taimakonsa da yayi har ya gano gaskiya, ya koka game da yadda matarsa ta zabi yaudararsa duk da irin yadda ya aminta da ita da zuciya daya.

"Na yarda da ita da zuciya daya da dukkan ruhina. Na tsaya tare da ita a dukkan ciwukanta da matsalolinta, amma ga abun da tayi na cin amana gare ni."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- A cewarsa.

Ya kara da cewa, dabi'unta sun janyo ya kamu da cutar.

"Tana shan maganin kanjamau, amma ni kuma na kamu da cutar. Bata damu ko in mutu ko kuma in rayu ba. Kenan, ni kawai hoto ne a wurin ta da za tayi amfani da shi..."

Martanin 'yan soshiyal midiya

Lebo ya ce:

"Da a ce namiji ne ya boye duk wannan, duniya za ta kama da wuta yayin da muke maganar nan, wannan 'dan uwa ne, uba, 'da kuma aboki ga wani."

Kara karanta wannan

Shekarun Diyata 4 Kacal: Magidanci Dan Shekaru 50 Ya Koka Kan Rashin Aure Da Wuri

Thabo_William ya ce:

"Ko sau nawa za mu yi adalci da wannan, aure ana gina shi ne kan gaskiya a matsayin ginshiki. Matar bata kyauta ba da ta boye hakan daga mijinta."

Mamngwevu ya ce:

"Zamu iya bada izurori ga wannan, amma ta fuskoki da dama hakan ba daidai bane. Tsawon shekaru uku. Ina mamakin mai zai faru idan matar ce ta gano hakan, besizothini?

margie7303 ta ce:

"Akwai bukatar muji daga gareta farko, sannan ka dena ganin hakan a matsayin abun kunya duk irin haushin da kaji, ta tsaya tare da ita, mutane na rayuwa da shi sama da shekaru 50.

YM Lilgee ya ce:

"Mutumi akwai bukatar ta natsu. Baka kamu da cutar ba, idan har tata cutar ba ta dauka bace, akwai yuwuwar kai da yaran bakwa da cutar. Tana bukatarka mana. Akwai bukatar ka san ko lafiyarta lau.”

Magidanci ya gane ba shi ne mahaifin dukkan yaransu ba

Kara karanta wannan

Bidiyo: Dumu-dumu Saurayi Ya Kama Budurwarsa Tana Masa Sata, Tayi Borin Kunya Kiri-kiri

A wani labari na daban, wani magidanci ya sanar da cewa bankado sirri wata hira tsakanin matarsa da wanda suke sharholiya yasa ya gane cewa dukkan yaran da suke da su ba nashi bane.

Kasancewarsa fitaccen mutum, yace kada a zargesa da rashin kula idan aka ga yaran a cikin halin fatara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel