Ministan FCT Wike Ya Mika Muhimmin Sako Ga Masu Filaye a Abuja

Ministan FCT Wike Ya Mika Muhimmin Sako Ga Masu Filaye a Abuja

  • Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Neysom Wike, ya bukaci duk wasu masu filaye a Abuja da su yi rijistar takardar mallakar fili ta C of O
  • Ya ce dai-daikun mutane za su biya naira dubu hamsin domin mallakar takardar ta C of O, yayin da kamfanoni za su biya naira dubu dari
  • Idan kamfani ba shi da NIN kuma suna da fili, dole su sanya lambar BVN, cewar Wike yayin da ya ke jaddada cewa kowa sai ya mallaki takardar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya umurci duk wani mai takardar shaidar mallakar fili (C of O) a Abuja ya sabunta takardar.

Kara karanta wannan

Wike ya magantu kan yiwuwar karawa da Tinubu a zaben 2027

Da ya ke jawabi a wani shirin kai tsaye na gidan talabijin a Abuja, Wike ya ce ana bukatar mutum ya gabatar da takardar dan kasa (NIN) da kuma lambar mallakar asusun banki (BVN) domin sabunta takarar ta C of O.

Nyesom Wike/Ministan Abuja
Ministan ya ce tun bayan fara aiki, ya daina sa hannu kan takardun C-of-O saboda ya fahimci akwai bukatar samar da matakan tsaro/. Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Ministan ya ce tun bayan fara aiki, ya daina sa hannu kan takardun C-of-O saboda ya fahimci akwai bukatar samar da matakan tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dai-daikun mutane za su biya naira dubu hamsin domin mallakar takardar ta C of O, yayin da kamfanoni za su biya naira dubu dari.

Me zai faru da wadanda dama suna da takardar C-of-O?

Ya ce :

"Akwai sabani da yawa, buga takardun C-of-O na bogi, don haka muka bullo da dabarar amfani da NIN idan za a nemi sabuwar takardar, wannan mataki ne mai kyau."

Kara karanta wannan

Daraktan kamfen PDP ya yi murna bayan shan kaye da PDP ta yi a kotu? gaskiya ta fito

"Idan kamfani ba shi da NIN kuma suna da fili, dole su sanya lambar BVN. Wannan zai tilasta wadanda ada ba su yi rijista ba yanzu su je su yi."

Ga wadanda suke da shaidar mallakar filayen tun-tuni, Wike ya ce dole su ma za su biya wani kudi domin sabunta takardar, cewar rahoton Premium Times.

Janar Kure da ya jagoranci murkushe Maitatsine ya kwanta dama

A wani labarin, babban kwamanda janar na rundunar soji, Yerima Kure (mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe shekaru 84 a duniya, Legit Hausa ta ruwaito.

Janar Yohanna Kure shi ne ya jagoranci dakarun soji wajen murkushe Maitatsine da jama'arsa a Kano a shekarar 1980 da kuma a Yola a shekarar 1982.

Asali: Legit.ng

Online view pixel