Ta baci: Sojoji da 'yan sanda sunyi musayar wuta
- An ruwaito cewa rikici ya kaure tsakanin yan sanda da sojoji wanda hakan ya haifar da musayar wuta tsakaninsu
- Rikicin ya tayar da hankalin mutane har ta kai ga al'umma suna barin ababen hawansu da shaguna suna gudu don tsira da rayukansu
- Sai dai har yanzu ba'a san takamamen abinda ya hadasa rikicin ba
An ruwaito cewa wasu sojoji da ke atisayen Foward Operation Base a garin Aba na jihar Abia sunyi wata arangama da yan sanda inda su kayi wata mummunar musayar wuta.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Osisioma Ngwa daura da titin Enugu zuwa Fatakwal, musayar wutan nasu ya razana masu ababen hawa da masu shaguna har ma suka rika gudawa suna barin kayayakinsu.
KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram
Duk da cewa ba'a gano takamamen abinda ya hadasa rikicin ba a lokacin rubuta wannan rahoton, an ga motoccin yan sanda da sojoji masu sintiri a hanyar Aba zuwa Owerri suna kokarin zuwa inda abin ke faruwa.
Yan sanda da sojoji da aka tuntuba a don jin ba'asi game da barkewar rikicin basu bayar da wani bayyani ba.
Sai dai kwamishan yan sanda na jihar Abia, Mr. Anthony Ogbizi ya ce a halin yanzu ba'a bashi rahoto game da afkuwar rikicin ba. "Ba dace inyi magana yanzu ba tunda ba'a gama bani cikaken bayani a kan abinda ya faru ba," inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng