Yadda Muka Sha Kaye a Zaben 1998 Domin Na Ki Bai Wa INEC Cin Hanci, Obasanjo

Yadda Muka Sha Kaye a Zaben 1998 Domin Na Ki Bai Wa INEC Cin Hanci, Obasanjo

  • Olusegun Obansanjo, ya bayyana yadda ya ki ba INEC cin hanci a zaben kananan hukumomin jihar Ogun a shekarar 1998, lamarin da ya ja jam'iyyar PDP ta sha kaye
  • Tsohon shugaban kasar ya ce sam bai ga dalilin da zai sa sai idan an yi amfani da tsarin "kudinka akwatinka" a zaben Najeriya ne mutum zai yi nasara ba
  • Obasanjo ya tuna yadda aka ba wani kudi don ya raba wa mutane, amma ya ki raba wa a inda ya dace, kuma ko a zaben majalisar jihar sai da PDP ta sha kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ogun- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya tuno yadda tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP ta sha kaye a zaben kananan hukumomi a jihar Ogun a shekarar 1998.

Kara karanta wannan

Cikakken bidiyon hirar Buhari ta farko bayan barin fadar shugaban kasa ya bayyana

Hakan kuwa ya faru ne saboda ya ki amincewa da shirin baiwa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) cin hanci.

Ya yi magana ne a Abeokuta a wani babban taron tuntuba da ya shirya kan ‘Sake nazari kan tsarin mulkin gwamnatin kasashen Yamma a kasashen Afrika'.

Olusegun Obansanjo
Tsohon shugabankar Najeriya Obasanjo ya ce bai amince a ba INEC cin hanci ba, lamarin da ya ja PDP ta fadi zaben kananan hukumomi a jihar Ogun a 1998. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bana jin dadin kalmar 'kudinka akwatinka', Obasanjo

Legit ta ruwaito Obasanjo na cewa shugabannin jam’iyyar sun gaya masa cewa ya kamata a ware kudi ga ‘yan sanda da kuma INEC.

Sai dai ya ki amincewa da shawarar bisa imanin cewa jami’an INEC da ‘yan sanda ma’aikatan gwamnati ne masu karbar albashi duk wata, Daily Trust ta ruwaito.

Ya shaida wa ’yan siyasa da farfesoshi a taron cewa ba ya jin dadin kalmar, ‘kudinka akwatinka’, yayin da ake tattaunawa kan dimokuradiyya da sauran batutuwan da suke kawo nakasu ga ci gaban kasar.

Kara karanta wannan

Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

A cewarsa, ya ci karo da kalaman ‘kudinka akwatinka’ a lokacin da al’ummar kasar suka gudanar da zaben kananan hukumomi na farko.

Ya kuma gano cewa, jam’iyyarsa ta sha kaye ne saboda ’yan siyasa sun ce ya ki amfani da tsarin "kudinka akwatinka" yayin da ake shirin gudanar da zaben.

Mutum mayunwaci na iya sayar da kuri'arsa kan naira 1,000, Obasanjo

Obasanjo ya ce:

“A lokacin zabe na gaba wanda shi ne na majalisar jiha, kawai na zauna a gidana, na ce ‘to, ku yi duk abin da kuke so, amma ba zan shiga ciki ba’.
Don haka, ni ban ma je ba, amma sakamakon haka ya sake kasance wa, mun sake shan kasa. Daya daga cikin wadanda suka karbi kudin bai ma raba inda ya kamata ya raba ba.”

Yayin da ya ke cewa lokaci ya yi da ya kamata a hankalta, tsohon shugaban kasar ya ce mai jin yunwa zai iya sayar da kuri’arsa kan naira 1,000 kacal.

Kara karanta wannan

Fani-Kayode ya caccaki Dino Melaye kan kayen da ya sha a zaben Kogi: “Allah Sarki Dino, ya zo na 3”

Darajar naira: Obasanjo ya ba Tinubu muhimmiyar shawara

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta haramta shigo da kayayyki daga kasashen waje, Legit Hausa ta ruwaito.

Olusegun Obasanjo ya na so a daina kawo tufafi da kayan Sin zuwa Najeriya domin a inganta tattalin arzikin kasa, labarin ya zo a jaridar Tribune.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel