Shari’ar Kano: Kuskuren da Aka Yi a Kotu Wajen Tsige Gwamna Abba Inji Femi Falana

Shari’ar Kano: Kuskuren da Aka Yi a Kotu Wajen Tsige Gwamna Abba Inji Femi Falana

  • Femi Falana ya dage cewa kotu ba tayi adalci wajen zaftare kuri’u fiye da 165, 000 a zaben gwamnan jihar Kano
  • Fitaccen lauyan yana ganin an zalunci masu kada kuri’a idan tsige wanda su ka zaba saboda laifin jami’an INEC
  • Falana SAN zai so a hukunta malaman hukumar zabe ne a maimakon ruguza kuri’un da Kanawa su ka kada

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shahararren lauya kuma mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana yana nan kan bakarsa a kan shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.

A ranar Litinin This Day ta rahoto Femi Falana SAN yana sukar salon da alkalai su ka dauka na rusa zabin da mutane su ka yi lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

A ra’ayin Femi Falana, babu dalilin azabtar da al’umma saboda kura-kuran malaman zabe.

Zaben Kano
An soki hukuncin zaben Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shari'ar zaben Kano, Filato da Zamfara

Lauyan ya yi wannan magana ne a yayin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a game da tsige gwamnonin Kano, Filato da Zamfara da aka yi.

A shari’ar Kano, kotun sauraron karar zabe da na daukaka kara sun ba APC da Nasir Gawuna nasara, aka tsige gwamnatin NNPP da ke kan mulki.

A shari’ar Zamfara an yarda da APC, an bukaci a sake zabe a wasu kananan hukumomi.

Falana ya ce abin da ya faru a shari’ar Legas ta sha bam-bam da abin da aka gani wajen yanke hukuncin zaben sabon gwamnan jihar Filato.

Femi Falana ya soki hukuncin Kano

"An fada mana a Filato an yi hukunci a kotun tarayya game da zaben tsaida gwanin da za ayi. An yi watsi kuma an sabawa umarnin, aka yi zabe a haka.

Kara karanta wannan

Jama'a sun hada-kai, sun yi karar Bola Tinubu a kotu kan nade-naden shugabannin INEC

Abin da ya saba da Kano, inda aka fada mana za a iya hukunta masu kada kuri’a. Tsari ne mai hatsari a hukunta jama’a saboda laifin malaman zabe.
An fada mana an yi asarar kuri’u 165, 000, saboda wasu malaman zabe sun yi kuskure da ba a buga hatimi ba. Ta ya hakan ya shafi kyawun zabe?
Ina fatan wannan karo kotun koli za ta gyara wadannan hayaniyan na rashin buga hatimin kuri’u malamanz aben da ya kamata a dauki mataki a kansu."

- Femi Falana SAN

Akwai hannun Tinubu a shari'o'in zabe?

Hukuncin da aka zartar a kotun daukaka karan ya shafi jam’iyyun adawa na NNPP da PDP ne, an ji hakan ya jawowa gwamnatin tarayya suka.

Bayo Onanuga ya yi maza ya wanke mai gidansa, ya ce Bola Tinubu bai da hannu a hukuncin, illa iyaka jam’iyyun sun sabawa dokar kasa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel