Jama'a Sun Hada Kai, Sun Yi Karar Bola Tinubu a Kotu Kan Nade-Naden Shugabannin INEC

Jama'a Sun Hada Kai, Sun Yi Karar Bola Tinubu a Kotu Kan Nade-Naden Shugabannin INEC

  • SERAP da BudgIT sun yi karar shugaban Najeriya saboda wasu mutanen da aka ba kujerar REC a hukumar INEC
  • Kungiyoyin da kuma wasu mutane sun dauki hayar lauyoyi zuwa kotu, su ka ce nade-naden ya ci karo da dokoki
  • An jefi shugaba Bola Tinubu da zargin dauko ‘ya ‘yan jam’iyyarsa ta APC, ya ba su alhakin gudanar da zabe na kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Kungiyoyin SERAP, BudgIT da wasu mutane 34 sun shigar da karar Bola Ahmed Tinubu a kotu saboda wadanda ya ba mukamai a INEC.

Premium Times ta ce nadin sababbin Kwamishinoni watau REC na hukumar INEC ya jawo magana, ana zargin an ba ‘yan siyasa aikin harkar zabe.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

Masu korafin sun ce daga cikin wadanda aka zaba su jagoranci INEC a shiyyoyin kasar nan, akwai wadanda ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Guinea Bissau Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga ciki akwai jami’an da aka tura zuwa jihohin Akwa Ibom, Edo, Legas da kuma Ribas, rahoto ya bayyana game da wannan tun kwanakin baya.

An kai Bola Tinubu kotu a Legas

A ranar Juma’a da ta gabata, karar mai lamba FHC/L/CS/2353/2023 ta isa Babban kotun tarayya da ke zama a Legas, ana neman soke nad-naden.

Lauyoyin da su ka shigar da kara sun bukaci a tursasawa shugaban kasa da shugaban majalisa cire ‘yan APC daga cikin Kwamishonin INEC.

Masu karar sun ce ba ‘ya ‘yan APC wannan mukami ya ci karo da doka, ya sabawa ka’ida kamar yadda aka ambata a sashe na 157 na tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

Rahoton ya ce masu karar sun nemi kotun tarayyar ta umarci shugaba Bola Tinubu ya nada mutane masu daraja da mutunci a kan kujerun REC.

A cewar lauyoyin da su ka je kotu; Kolawole Oluwadare da Andrew Nwankwo, dole wanda zai yi aiki da INEC ya zama adali mara goyon bayan kowa.

Shugaba Tinubu ya tura 'Yan APC INEC

"Daga cikin wadanda aka zaba kuma majalisar dattawa ta tantance a matsayin REC akwai wanda ‘dan PDP ne wanda ake zargin ya koma APC kuma ya yi aiki da Godswill Akpabio a lokacin ya na Gwamnan Akwa Ibom.
Akwai wadanda ake zargin sun goyi bayan zaben Tinubu kuma an taba ba shi mukami a 2001 a lokacin da Tinubu ya mulki jihar."

- Kolawole Oluwadare da Andrew Nwankwo

Tsohon Sanatan APC ya soki kotu

Tsohon Sanata a Kaduna ya ce kotu tana neman zama makarar da ake birne damukaradiyya a yau ganin hukuncin zaben gwamnan Filato.

Shehu Sani ya zargi Alkalai da fito da dabaru domin karbe mulki daga hannun ‘yan adawa ya ce soke nasarar gwamnan jihar Filato abin takaici ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel