Tashin Hankali Yayin da Mutane 13 Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Manoma da Makiyaya a Jihar Filato

Tashin Hankali Yayin da Mutane 13 Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Manoma da Makiyaya a Jihar Filato

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu tsaiko tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato
  • An labarta yadda aka samu mutuwar wasu mutane a jihar duk dai sakamakon wasu hare-hare a ranar Juma’a
  • Ya zuwa yanzu, hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar wasu daga cikin hare-haren da aka samu

Jihar Filato - Akalla mutane 13 ne aka kashe a wani sabon rikicin da ya barke a wasu yankunan karamar hukumar Barikin Ladi ta Jihar Filato a ci gaba da hare-haren ramuwar gayya tsakanin makiyaya da manoma.

Lamarin na baya-bayan nan ya faru ne kwana guda bayan da aka yi wa makiyaya biyar kwanton bauna a unguwar Rawuru da ke yankin Barikin Ladi, Daily Trust ta ruwaito.

Sa’o’i kadan bayan kashe makiyayan, rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a unguwar Rawuru inda suka bindige mutane har takwas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Yadda aka kashe mutane a Filato
Jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ban san da labarin kisan makiyaya ba

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred ya tabbatar da harin na biyu da aka kai wa mazauna yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ba shi da masaniya game da kisan da aka yi wa makiyayan, inda ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu a harin na dare ba.

A kalamansa:

“Bani da labarin kashe makiyayan amma an kai hari a unguwar Rawuru inda aka kashe mutane tare da kona gidaje. Mutanenmu suna can kuma muna jiran samun rahoton abin da ya faru.”

Martanin kungiyar makiyaya ta MACBAN

Sai dai shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar Nuru Abdullahi ya shaida wa Daily Trust cewa, tabbas a ranar Juma’ar da ta gabata an kashe wasu makiyaya biyar.

Nuru ya cen an kashe makiyayan ne yayin da suke dawowa daga kasuwar shanu da ke garin Bukuru ta karamar hukumar Jos ta Kudu, inda yace sun je kasuwar ne don sayar da shanunsu.

Kara karanta wannan

"Maganin Kara Kuzarin Maza Ya Sha": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka a Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa, Budurwar Ta Tsere

Ya kara da cewa:

“Kwamishanan ‘yan sanda ya sani. Hukumar DSS da Operation safe Haven sun sani. Dukkanin hukumomin tsaro sun sani.”

Kisa da satan mutane ya zama ruwan dare a Filato

Hare-hare dai sun zama ruwan dare, musamman tsakanin manoma da makiyaya a ‘yan kwanakin nan a jihar, inda bangarorin biyu ke zargin juna da ta’asar.

A watan Mayu, an kashe mutane da dama a karamar hukumar Mangu bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari a kauyukan yankin.

Garkuwa da mutane na daya daga cikin abubuwan da ke yawan faruwa a jihar ta Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel